MisbahuAbudullah 1
M.misbahu pic
Barka da zuwa
ShafimaiAlbarka

Wannan Shafi Yana Zuwa Muku ne Daga Dan Uwanku

Misbahu Abdullahi Al'athariy


→Home
→Rusa Kare rayin Sarkin Kogo
→Samuwar Ibn Saba'!
→Ba Anan Take Ba!!!
→Sarkin Copy And Paste
→Ahlul Bait Basa Ragawa Y'an Shi'a
→Addinin Shi'a
→Tattaunawa
→Watan Azumin Tsofaffi Sunnah & Bidi'a
→Karayar Mukabala a Misra
→Shi'anci Da Sufanci
→Un Categories




FITOWA TA )1(.
.
ABDULLAHI DAN UMAR YANA SON HALIFANCI, KUMA YANA DA RIGIMA DA MU'AWIYA KAN HAKA??.
.
* ABDULLAHI DAN UMAR YA SAMU SHAIDA DAGA GURIN MALAMAN TARIHI AKAN GUDUN MULKI DA JAGORANCI, ABU NU'AIM DAYAZO BAYANI KANSA SAI YACE:
ﻭﻣﻨﻬﻢ ﺍﻟﺰﺍﻫﺪ
ﻓﻲ ﺍﻟﺈﻣﺮﺓ ﻭﺍﻟﻤﺮﺍﺗﺐ...
DAGA CIKINSU -SAHABBAI- AKWAI MAI GUDUN SHUGABANCI DA JAGORANCI- IBN UMAR-.
DUBA: HILYATUL AULIYA'I 1/326.
.
WANNAN SAI YAKE NUNA MANA CEWA: DA'AWAR YANA SON JA GORANCI DA'AWACE KAWAI TA SHUGABAN YA'N KO WAYE.
.
* ZAHABI YAKAWO RUWAYA CEWA ANZO AN SAMI IBN UMAR ANCE YAZO AYI MASA MUBAYI'A, SAI YACE BA YA SO.
DUBA: SIYAR 3/215,
.
** IBN UMAR BAI SAMU WANDA ZAI NADA SHI BANE AMMA YANA BALA'IN SON KUJERAR DA MU'AWIYA YAKE KAI???.
.
DALILAN DAKE KARYATA WANNAN DA'AWAR GASU KAMAR HAKA:
.
1: ZAHABI YAKAWO CIKIN SIYAR 3/225:
IBN UMAR YACE:
ﺑﻌﺚ ﻟﻲ
ﻋﻠﻲ , ﻓﻘﺎﻝ: ﺍﻧﻚ ﻟﺮﺟﻞ ﻣﻂﺎﻉ ﻓﻲ ﻫﻞ ﺍﻟﺸﺎﻡ ,ﻓﺴﺮ ﻓﻘﺪ ﻣﺮﺗﻚ ﻋﻠﻴﻬﻢ, ﻓﻘﻠﺖ: ﺫﻛﺮﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻗﺮﺍﺑﺘﻲ ﻣﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - ﻭﺻﺤﺒﺘﻲ ﻟﺎ ﻣﺎ ﻋﻔﻴﺘﻨﻲ, ﻓﺄﺑﻰ ﻋﻠﻲ, ﻓﺎﺳﺘﻌﻨﺖ ﻋﻠﻴﻪ ﺑﺤﻔﺼﺔ ﻓﺄﺑﻰ....
-SAYYIDNA- ALIYYU YA AIKA KIRANA, SAI YACE: NAGA MUTANEN SHAM SUNA YI MAKA BIYAYYA; DON HAKA KAJE NA NADA KA SHUGABANCINSU.
.
SAI NACE MASA: KATUNA UBANGIJI, DA KUSANCI NA DA ANNABI )S.A.W( DA MATSAYIN SAHABBANTAKA DANAKE DASHI, KASAUWAKE MIN WANNAN LAMARIN. SAI -S.ALI- YAKI YARDA, SAI NANEMI TAIMAKON HAFSA- TASA BAKI YARABU DANI- AMMA SAI YAQI AMINCEWA......".
.
WANNAN YA ISA YAQARYATA CEWA IBN UMAR BAI SAMI WANDA ZAI NADA SHI BANE.
.
2: BALMA IBN UMAR YANA CIKIN WADANDA SUKAYIWA MU'AWIYA MUBAYI'A LOKACIN DA AL'AMARI YAZO HANNUNSA, TAYAYA KUMA ZA ACE AKWAI QULLALLIYA TSAKANINSA DA MU'AWIYA??
.
IBN HAJAR YACE:
ﻭﺑﺎﻳﻊ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻣﻌﺘﺰﻟﺎ ﻟﻠﻘﺘﺎﻝ, ﻛﺎﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻭﺳﻌﺪ ﺑﻦ ﺑﻲ ﻭﻗﺎﺹ ﻭﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻣﺴﻠﻤﺔ.
WADANDA SUKAQI SHIGA CIKIN YAQIN- BASU TAYA S. ALI BA BAKUMA SU TAYA S. MU'AWIYA BA- SUN YIWA MU'AWIYA MU'AWIYA MUBAYI'A- LOKACIN DA KALMA TAHADU KANSA-, KAMAR IBN UMAR DA SA'AD BN ABIY WAQQAS DA MUHAMMAD BN MASLAMATA.
DUBA : FAT'HUL BARI 13/84.
.
*ABUN LURA ANA BIYU NE:
.
1: IBN UMAR YANA DA MATSALA DA MU'AWIYA AMMA KUMA YAQI TAIMAKAWA ALIYU A YAQI MU'AWIYAN???
.
2: YA AKAYI KUMA YAIWA MU'AWIYAN MUBAYA'A BAYAN YANA GABA DA MULKINNASA??
.
** 3: IBN UMAR YA YABI MU'AWIYA YACE: YA IYA JAGORANCI, .
.
ZAHABI YACE:
ﻭﺃﺛﻨﻰ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺑﺄﻧﻪ ﺳﻮﺩ ﺍﻟﻨﺎﺱ.
SIYAR 5/128.
.
*** KAFA HUJJA DA HADISIN:
ﻣﻦ
ﻛﺎﻥ ﻣﺘﻐﻠﺒﺎ ﻓﻲ ﻫﺬ ﺍﻟﺄﻣﺮ.
ACIKI IBN UMAR YACE:
ﻣﺎ ﺣﺪﺛﺖ ﻧﻔﺴﻲ ﺑﺎﻟﺪﻧﻴﺎ ﻗﺒﻞ ﻳﻮﻣﺌﺬ.
ZUCIYATA BATA TABA RAYA MIN SON DUNIYA BA KAFIN WANNAN RANAR.
&** AMSA:
WANNAN LAFAZIN BAI INGANTABA., TAZO NE TA:
ﺣﺒﻴﺐ ﺑﻦ ﺑﻲ ﺛﺎﺑﺖ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ.
WANDA KUMA HABIB DINNAN YANA YAWAN TADLISI KUMA YA KAWOTA DA LAFAZIN "AN".
YAZO CIKIN: ﺗﻌﺮﻳﻒ ﻫﻞ ﺍﻟﺘﻘﺪﻳﺲ SHAFI NA: 35 LAMBA69:
ﺣﺒﻴﺐ ﺑﻦ ﺑﻲ ﺛﺎﺑﺖ ﺍﻟﻜﻮﻓﻲ ﺗﺎﺑﻌﻲ ﻣﺸﻬﻮﺭ ﻳﻜﺜﺮ ﺍﻟﺘﺪﻟﻴﺲ.
DON HAKA WANNAN LAFAZIN BAI INGANTABA.
.
** SAURAN BAYANI GAMEDA WANNAN HADISIN DA SAURAN HUJJAR SHUGABAN YA'N KOWAYE ZAI ZO ARUBUTU NAGABA.




FITOWA TA )2(.
.
ABDULLAHI DAN UMAR YANA RIGIMA DA MU'AWIYA AKAN MULKI.
.
CI GABA!!
.
KAMAR YANDA YAGABATA MUNJI CEWAR DA'AWAR IBN UMAR YANA SON MULKI DA'AWACE BA DAIDAI BA, KAMAR YANDA MUN KAWO HUJJOJI DAKE RUSA TA.
SANNAN BATUN CEWA IBN UMAR BAI SAMU WANDA ZAI NADA SHI BANE ITAMA BA DAI DAI BANE, DOMIN MUN KAWO INDA HAR NADA SHI AKAYIMA AMMA YAQI AMINCEWA.
.
ZAMU DORA::
.
SHUGABAN YAN KOWAYE SAI YACE:
.
" MU 'AWIYA YA TASHI YAYI HUDUBA YANA GANIN CEWA SUNA JIN TSORONSA BAZA SU IYA AMSA MASABA....".
.
* WANNAN BATUN NASA KAMAR YANA SO YANUNA CEWA MU'AWIYA YANA JIN KANSA YANA GANIN BAZA A IYA FADA MASA GASKIYA BA;
SABODA GIRMAN KAI, WANDA KUMA QARYA CE YAYIWA MU'AWIYA- ALLAH KUMA ZAI SAKA MASA KAN HAKA-.
.
ABUNDA ZAI KARYATA WANNAN KARYAR ATAKAICE:
.
** IMAMU AHMAD YA KAWO ACIKIN AZZUHDU CEWA ABU MUSLIM YA KWALAWA MU'AWIYA KIRA YANA ZAUNE AKAN MINBARI YACE DASHI:
ﺃﻧﺖ ﻗﺒﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ...
HAR ZUWA KARSHEN RUWAYAR, BAYAN YA KAMMALA SAI MU'AWIYA YAFUSKANCESHI YACE MASA:
ﻳﺮﺣﻤﻚ ﻳﺮﺣﻤﻚ ﺍﻟﻠﻪ.
WANDA KUMA YA FADA MASA MAGANGANUNDA DA ACE MU'AWIYA YANA DA GIRMAN BA YANDA ZA AYI YANUNA GODIYARSA GAME DA ABUNDA YAFADA MASA.
.
** RUWAYA TAZO CEWA:
MU'AWIYA YAYIWA WADANDA KE TARE DASHI TAMBAYA AMMA BASU AMSA BA, YASAKE MAIMAITAWA AKARO NADABAN BASU BASHI AMSA BA, AKARO NA UKU SAI WANI YATASHI YABASHI AMSA, SAI MU'AWIYA YAKA MO HANNUNSA YASHIGO DASHI FADARSA YAI MASA GODIYA, YACE MASA KA TSERATAR DANI.
SAI MUKA FAHIMCI ASHE MU'AWIYA MURNA YAKE DAYA SAMU WANDA ZAI FADA MASA GASKIYA, AMMA KAI KUMA KAZO KA SHARARA MASA KARYA.
****
.
HUJJAR SHUGABAN YA'N KOWAYE, KAN CEWA IBN UMAR YANA KWADAYIN MULKI:
.
)1( HADISIN:
ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻣﺘﻐﻠﺒﺎ ﻓﻲ ﻫﺬ ﺍﻟﺄﻣﺮ ﻓﻠﻴﻂﻠﻊ ﻟﻨﺎ ﻗﺮﻧﻪ:
AMSA:;
.
1: MALAMAI SUNYI SABANI GAME DA LOKACINDA HAKAN YAFARU KAMAR HAKA:
.
* HAKAN YA FARU NE LOKACINDA MU'AWIYA YASO NADA DANSA YAZIDU WALIYYUL AHAD- SHUGABA MAI JIRAN GADO-,, WANNAN KUMA RA'AYIN IBNUL JAUZIY NE.
.
IBN HAJAR KUMA YACE: WANNAN RA'AYIN BABU HUJJA KANSA.
ﻛﺬﺍ ﻗﺎﻝ, ﻭﻟﻢ ﻳﺄﺕ ﻟﻪ ﺑﻤﺴﺘﻨﺪ.
DUBA: FAT'HUL BARI 7/511.
.
** HAKAN YA FARU NE A DAUMATUL JANDAL, WANDA KUMA YAZONE TA RUWAYAR HABIB BN ABIY SABIT, KAMAR YANDA DABARANIY YAKAWO.
.
ARUBUTUN BAYA KUMA MUNYI MAGANA KAN RASHIN INGANCIN RUWAYAR.
.
*** HAKAN YA FARUNE BAYAN LAFAWAR KURA TSAKANIN S.ALI DA S. MU'AWIYA- BAYAN TAHKIM-.
WANNAN KUMA RA'AYIN IBN HAJAR NE.
.
IDAN MUKA TAFI KAN CEWA HAKAN YA FARUNE BAYAN TAHKIM SAI NACE:
.
1: RUWAYOYI SUN NUNA CEWA MAGANAR TAHKIM DA AKE BAWAI AKAN MULKI BANE, ANA YINTA NE GAME DA SHAWO KAN MATSALAR SABANIN DA AKA SAMU GAME DA WANDA SUKA KASHE USMAN; DON HAKA BATUN ACE MU'AWIYA AKAN MULKI YAYI KHUDUBAR KENAN ZAI ZAMA ABUN DUBAWA.
.
ANAN MASU GANIN CEWAR MU'AWIYA YANA MAGANANE KAN CEWA WANE YAFISHI CANCANTA DA JININ S. USMAN, SHI KUMA IBN UMAR BAI FAHIMCI ME YAKE NUFI BA HAR YAKUSA TANKAWA KUMA SAI YAFASA, WANNAN MAGANAR ZATA ZAMA ABAR DUBAWA KENAN.
.
2: FADIN MU'AWIYA:
ﻓﻠﻨﺤﻦ ﺣﻖ ﺑﻪ ﻣﻨﻪ ﻭﻣﻦ ﺑﻴﻪ.
IDAN KACE: AI DA IBN UMAR YAKE, SAI NACE MAKA:
IBN HAJAR YA RUSA WANNAN HANGEN,YACE:
ﻓﻴﻪ ﺑﻌﺪ,ﻟﺄﻥ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﻛﺎﻥ ﻳﺒﺎﻟﻎ ﻓﻲ ﺗﻌﻆﻴﻢ ﻋﻤﺮ.
BALMA MU'AWIYA BA YA KWATANTA KAMSA DA IBN UMAR WAJEN FALALA. YA ZO CIKIN TARIKU DIMASHQ 59/163,, MU'AWIYA YACE:
ﻭﺇﻥ ﻣﻨﻜﻢ ﻟﻤﻦ
ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻨﻲ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ...
"ACIKINKU AKWAI WANDA YAFINI ALKAIRI SHINE IBN UMAR.
.
IDAN KUMA KACE: DA ALIYYU KUMA MULKI YAKE NUFI, SAI NACE MAKA:
YAZO CIKIN TARIKH NA DABARIY 3/77,, MU'AWIYA YA RUBUTAWA ALIYYU YACE: KABAMU WADANDA SUKA KASHE USMAN AYI MUSU HUKUNCI MU KUMA ZAMUFI KOWA SAURIN AMSA KIRANKA DAYIMAKA DA'A.
.
ASHE KENAN BAI FADA DASHI KAN MULKI BA.
DUBA: ASSIQAT NA IBN HIBBAN 2/287.
.
YA ZO CIKIN FATHUL BARI 13/86,
DA ALBIDAYA TA IBN KASIR 8/129: MU'AWIYA YACE:
ﻟﺎ
ﻧﺎﺯﻋﻪ
ﻓﻲ ﺍﻟﺨﻠﺎﻓﺔ ﻭﺇﻧﻲ ﺃﻋﻠﻢ ﻧﻪ ﻓﻀﻞ ﻣﻨﻲ.
NIFA BA NA JAYAYYA DA- ALI- AKAN HALIFANCI, NI KAINA NA SAN YA FINI FALALA.
.
DON HAKA BATUN CEWA MULKI YAKE NEMA BA DAI DAI BANE.
.
**** ANAN NAKE QALUBALANTAR SHUGABAN YA'N KOWAYE AKAN CEWA FADINSA:
.
"" IBN UMAR YA TASHI YANA TIMA YA ZAGI IBN UMAR""
.
KARYA YAKE YI DUK LAFUZZAN RUWAYAR WADANDA SUKA INGANTA DA WADANDA BASU INGANTABA BABU INDA AKA KAWO HAKA IDAN KUMA AKWAI YANUNA GURIN.
.
ZAMU CIGABA




FUTOWA TA )3(.
.
ABDULLAHI IBN UMAR YANA RIGIMA DA MU'AWIYA AKAN SHUGABANCI.
.
KARKARE WANNAN MAS'ALAR.
DALILI NABIYU DA SHUGABAN YA'N KOWAYE YA KAWO GAMEDA WANNAN MAS'ALAR.
ﻟﺎ ﺭﻯ ﻟﻬﺬ ﻏﻴﺮ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ, ﻓﻬﻞ ﻟﻚ ﺃﻥ ﺗﻌﻂﻰ ﻣﺎﻟﺎ ﻋﻆﻴﻤﺎ ﻋﻠﻰ ﺗﺪﻉ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺄﻣﺮ ﻟﻤﻦ ﻫﻮ ﺃﺣﺮﺹ ﻋﻠﻴﻪ ﻣﻨﻚ....
AMRU YACE: NI FA INA GANIN BABU WANDA YADACE DA WANNAN MATSAYIN SAI IBN UMAR.. SAI AMRU YACEWA IBN UMAR DIN: SHIN ZAKA IYA YADDA ABAKA DUKIYA MAI TARIN YAWA DOMIN KABARWA WANDA YAFIKA SON WANNAN KUJERAR??
.
SAI IBN UMAR YAYI FUSHI YATASHI ZAI FITA.
.
*SAI SHUGABAN KOWAYE YACE:
.
WANNAN DALILI NE DAKE NUNA CEWA IBN UMAR YANA SON MULKI, KUMA YANA DA RIGIMA DA MU'AWIYA AKAN KUJERAR SHUGABANCI.
.
******** AMSA GAME DA KAFA HUJJA DA WANNAN RUWAYAR.
ZAMU KAWAR DA KAI GAMEDA DIRASAR SANADIN RUWAYAR, MUTAFI ZUWA GA LAFAZINNATA DA ABUNDA TAKE NUNAWA.
.
** IBN ASAKIR YA KAWO TA CIKIN TARIKHU DIMASHQ LAMABA TA 31220, DA LAFAZIN:
ﻟﺎ
ﺩﺭﻱ ﻟﻬﺬﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ
.
ZAHABIY YA KAWO TA CIKIN TAZKIRA.
DA LAFAZIN:
ﻟﺎ
ﺃﺭﻯ. HAKA KUMA LAFAZIN YAKE CIKIN HILYATUL AULIYA'I 1/328.
.
1: WANNAN RUWAYAR BABBAN ABUNDA TAKE NUNAWA SHINE:
.
YANDA ABDULLAHI IBN UMAR YAKE GUDUN JAGORANCI DA MULKI SABANIN YANDA SHI WANCAN MUTUMIN YAYI DA'AWA.
AKARSHEN RUWAYAR GA ABUNDA YACE:
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ
ﻋﻂﻲ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﻭﻟﺎ
ﺃﻗﺒﻞ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﻭﻟﺎ ﻓﻌﻠﻬﺎ ﺇﻟﺎ ﻋﻦ
ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ
" WALLAHI BAZAN BADA KOMAI AKAN ABANI MULKI BA, BA KUMA ZAN KARBI WANI ABU DON NAYI MULKI BA, BAKUMA ZANYI MULKINMA BA SAI DA YARDAR MUSULMI".
.
AWANI LAFAZIN:
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ ﻋﻂﻲ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺷﻴﺌﺎ ﻭﻟﺎ ﻋﻂﻰ ﻭﻟﺎ ﻗﺒﻠﻬﺎ ﻟﺎ ﻋﻦ ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ.
WANNAN KARASHEN RUWAYAR KADAI YA QARYATA DA'AWAR SHUGABAN YA'N KOWAYE, SHI YASA MA YAKI YARDA YAKAWO KARASHEN RUWAYAR, WANDA KUMA WANNAN HA INCI NE.
.
2: DALILIN DA YASA IBN UMAR YAYI FUSHI SHINE YANA KOMAWA NE ZUWA GA ABUNDA YAJI AN FADA MASA NACEWAR ZAI IYA BADA KUDI AKAN AZABESHI SHUGABA, SHI KUMA SAI YA FUSATA YATASHI ZAI FITA KAMAR YANDA YAZO CIKIN LAFAZIN DA ZAHABIY YAKAWO CIKIN TAZKIRA:
ﺗﻌﻂﻴﻨﻲ ﻣﺎﻟﺎ ﻋﻠﻰ ﺑﺎﻳﻌﻚ
ZA KA IYA BANI KUDI KUWA AKAN NAYI MAKA BAI'A??
.
AWANI LAFAZIN KUMA:
ﻧﻌﻂﻰ ﻣﺎﻟﺎ ﻋﻠﻰ ﻧﺒﺎﻳﻌﻚ
ZAKA YARDA ABAMU KUDI KAN MUYI MAKA MUBAYA'A??
.
KUMA DUKKAN LAFUZZAN RUWAYAR AKARSHENTA SUN NUNA ABUNDA AKE NUFI KENAN, AMMA SABODA RASHIN TSORON ALLAH WANCAN MUTUMIN SAI YACE WAI IBN UMAR YAYI FUSHI SABODA KAWAI YAJI ANCE ZAI IYA KARBAR KUDI KUWA YAHAKURA DA KUJERAR.
.
3: SU KANSU MASU MAGANAR KAMAR YANDA RUWAYAR TANUNA SUN TABBATAR CEWA IBN UMAR BAYA SON JAGORANCI, SHI YASA MA AMRU AKARSHE YACEWA IBN UMAR BAYAN YAJI AMSAR DA TAFITO DAGA BAKIN IBN UMAR DIN:
ﻧﻤﺎ ﻗﻠﺖ ﺟﺮﺑﻚ
"NA FADA NE FA KAWAI DON NA GWADA KA".
.
ATAKAICE DAI MUN FAHIMCI ABUBBA KAMAR HAKA:
.
1: DA'AWAR CEWA IBN UMAR YANA SON MULKI QARYA NE.
2: DA'AWAR YANA RIGIMA DA MU'AWIYA KAN MULKI QARYA NE.
3: BATUN CEWA IBN UMAR BAI SAMU WANDA ZAI BASHI MULKI BANE AMMA YANA BALA'IN SO KARYA NE.
4:MU'AWIYA YANA GANIN CEWA IDAN YAFADI MAGANA BAZA'A IYA AMSA MASABA SHIMA QARYA NE.
5: IBN UMAR YA TASHI YA ZAGI MU'AWIYA AGABAN JAMA'A QARYA NE BA INDA AKAI HAKA.
6: HUJJOJIN DA SHUGABAN KOWAYE YAKAFA HUJJA DASU KAN WADANNAN DA'AWOYINNASA BA SHI DA HUJJA CIKINSU KAMAR YANDA BAYANI YAGABATA.
.
*** WANNAN ITACE NUQDAR FARKO DA SARKIN GIDA YATAUNA ACIKIN RADDIN NASA; MUN KUMA BA DA AMSOSHI KANTA, ZA MU TSALLAKA NUQDA TAGABA.
.
ZAMU CIGABA!!



FUTOWA TA HUDU )4(.
.
ME YASA SU NANA AISHA SUKA FITO YAKIN JAMAL BAYAN SUN TABBATAR S. ALIYYU BA SHI DA HANNU CIKIN KISAN S. USMAN??
.
ANYA BA WATA MANUFA SUKE DA ITA ABOYE BA??
.
WANNAN ITACE TUHUMAR DA SARKIN GIDA YAYI ACIKIN KASET DINSA, YAKAFA HUJJA DA FADINSA:
.
YA ZO CIKIN TARIKHUL UMAM, AHNAF BN QAIS YACE:
ﺇﻧﻲ ﻟﺎ ﺭﻯ ﻫﺬ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻟﺎ ﻣﻘﺘﻮﻟﺎ
NI KAM FA INA GANIN WANNAN MUTUMINFA-USMAN- KASHE SHI ZA AYI..
ﻓﺄﺗﻴﺖ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻓﻘﻠﺖ ﻣﻦ ﺗﺄﻣﺮﻳﻨﻨﻲ ﺑﺎﻳﻊ
SAI NAJE GURIN A'ISHA NACE MATA: WA ZAKI UMARCE NI NAYIWA MUBAYI'A- BAYAN AN KASHE USMAN-?
.
SAI TACE MASA: ALIYYU ZAKAIWA MUBAYI'A.
.
AMSARMU GAME DA TUHUMARSA.
.
*FADAKARWA:
.
A MANHAJINMU SAHABBAI BA MA'ASUMAI BANE ZASU IYA AIKATA KUSKURE,M; SABODA YA'N ADAMTAKA; DON HAKA ZAKA SAMU MALUMANMU SUNA TABBATAR DA CEWA WANNAN SABANIN DA YA FARU TSAKANIN SAHABBAI DA S. ALIYYU TO S. ALIYYU SHINE AKAN DAI DAI, WADANDA KUMA SUKA SABA MASA IJTIHADI SUKAYI KUMA SUKAYI KUSKURE.
.
1: WANNAN ASAR DIN DABARI YA KAWO SHI DA SANADINSA,
WANDA BAZAN TSAWAITA BA KANSA, SABODA GUDUN TSAWAITAWA.
.
IBN HAJAR YA KAWO TA CIKIN FAT'HUL BARI 13/46-47.
.
2: BABBAN ABUNDA WANNAN ASAR DIN KE NUNAWA SHINE: SAHABBAI ASHE BASUYI FADA DA S. ALIYYU DON SON RAI BA, BAL SUNYI IJTIHADINE SUKAYI KUSKURE, TUNDA GA SHI HAR SU DAKANSU SUKE CEWA IDAN AN KASHE S. USMAN TO S. ALI YAKAMATA AYIWA MUBAYI'A; DON HAKA IDAN SUNA KINSA NE KAMAR YANDA SHUGABAN MAKARANTAR KOWAYE YAKE NUNAWA BAZA SUYI NUNI ZUWA GA ZABAR SABA.
.
3: ABUNDA KUMA YASA NANA AISHA TA FITO YAKIN JAMAL GA SHINAN:
.
NANA AISHA TA RUBUTAWA ABU MUSA- WANDA S. ALI YANADA GWAMNAN KUFA- TACE DASHI:
ﻓﺈﻧﻪ ﻗﺪ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻗﺘﻞ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﻣﺎ ﻗﺪ ﻋﻠﻤﺖ,
"KA SAN DAI MAI YA FARU GAMEDA KISAN USMAN"
ﻭﻗﺪ ﺧﺮﺟﺖ ﻣﺼﻠﺤﺔ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ
** NI KUMA GA SHI NA FITO DON YIN SULHU TSAKANIN MUTANE***
ﻓﻤﺮ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻚ ﺑﺎﻟﻘﺮﺍﺭ ﻓﻲ ﻣﻨﺎﺯﻟﻬﻢ
DON HAKA KA UMARCI JAMA'AR GURINKA SU ZAUNA AGIDAJENSU.
ﻭﺍﻟﺮﺿﺎ ﺑﺎﻟﻌﺎﻓﻴﺔ
SU KUMA YARDA SU ZABAWA KAMSU ZAMAN LAFIYA
ﺣﺘﻰ
ﻳﺄﺗﻬﻢ ﻣﺎ ﻳﺤﺒﻮﻥ ﻣﻦ ﺻﻠﺎﺡ ﻣﺮ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ
HAR SU SAMI ABUNDA SUKE SO NA DAI DAITUWAR LAMURRAN MUSULMI.
.
DUBA: sahih na ibn hibban 15/126,, lamba 6732.
.
DON HAKA ASHE ITA SULHU NE YAFITO DA ITA KENAN BA YA KI BA.
.
ZAMU CIGABA !!
.
FUTOWA TAGABA:
.
DALHA YANA DA HANNU CIKIN KISAN USMAN.




FITOWA TA )5(.
.
WADANDA SUKE CEWA JININ S. USMAN SUKE NEMA SUNE SUKA KASHE S. USMAN DIN.)WANENE YAKASHE DALHA??(
.
WANNAN DA'AWAR ITA SARKIN GIDA YAYI BAYAN YA KAFA HUJJA KAMAR HAKA:
.
*YAZO CIKIN SIYAR 28/255.
.
MARWAN YA KALLI DALHA RANAR YAQIN JAMAL ,SAI YACE:
ﻟﺎ ﻃﻠﺐ ﺛﺄﺭﻱ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﻴﻮﻡ,ﻓﺮﻣﻰ ﻃﻠﺤﺔ ﺑﺎﻟﺴﻬﻢ ﻓﻘﺘﻠﻪ.
"NI KAM BA NA NEMAN WATA FANSA TA JININ S. USMAN, SAI YAJEFI DALHA DA MASHI YAKASHESHI".
.
** DAKUMA FADINSA:
.
MARWAN YA FADAWA DAN S. USMAN:
ﻗﺪ ﻛﻔﻴﻨﺎﻙ ﺑﻌﺾ ﻗﺘﻠﺔ ﺑﻴﻚ
HAKIKA MUN ISAR MAKA- MUNYI MAKA AIKI- GAME DA BANGARE NA WADANDA SUKA KASHE MAKA BABANKA".
.
KUMA ALHALIN DALHA YANA CIKIN WADANDA SUKE DA'AWAR NEMAN FANSAR JININ S. USMAN, SAI GASHI MA'AIKACI AGIDAN S. USMAN DIN YA CE DALHA DINNE YAKASHE SHI; DON HAKA DAMAN MASU CEWA JININSA SUKE NEMA SUNE DIN SUKA KASHESHI DASUKAGA ZATA KAWABE SAI SUKA FITO SUNA DA'AWAR JININSA SUKE NEMA.
.
AMSA GAMEDA WANNAN TUHUMAR TASA:
.
1: RUWAYAR DKA KAWO TAFARKO
ﻟﺎ
ﻃﻠﺐ ﺑﺜﺄﺭﻱ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﻴﻮﻡ
BAGAWI YA KAWO TA CIKIN MU'UJAM NA SAHABA 3/411. BATA INGANTA BA KUMA SABODA ABUBBA KAMAR HAKA:
.
* AKWAI QATADA BN DI'AMAH ASSADUSIY ACIKIN ISNADINTA, WANDA KUMA YANA TADLISI, KUMA BAI SARRAHA SAMA'INSA DAGA JARUD BA.
YAZO CIKIN: ﺗﻌﺮﻳﻒ ﻫﻞ ﺍﻟﺘﻘﺪﻳﺲ SHAFI 35,, LAMBA TA 92:
ﻗﺘﺎﺩﺓ ﺑﻦ ﺩﻋﺎﻣﺔ
HAFIZ YACE:
ﻛﺎﻥ ﺣﺎﻓﻆ ﻋﺼﺮﻩ, ﻭﻫﻮ ﻣﺸﻬﻮﺭ ﺑﺎﻟﺘﺪﻟﻴﺲ.
** ﺟﺎﺭﻭﺩ ﺑﻦ ﺑﻲ ﺳﺒﺮﺓ YANA QARAMI SANDA KISSAR TAFARU; DON HAKA BAI HALACCI YAKIN JAMALBA, BARE KUMA YABADA LABARIN ABUNDA YAFARU ACAN.
SANNAN N RUWAITO TA DA LAFAZIN:
ﻟﺎ ﺩﺭﻙ ﺑﺜﺄﺭﻱ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﻴﻮﻡ
HAKIM YA KAWO TA CIKIN MUSTADRAK3/417.
BATA INGANTA BA KUMA SABODA JAHALAR SHARIKH DA UTBAH.
2: RUWAYA TABIYU:
ﻗﺪ ﻛﻔﻴﻨﺎﻙ ﺑﻌﺾ ﻗﺘﻠﺔ ﺑﻴﻚ.
AN RUWAITO TA DA LAFAZIN ﺣﺪ ﻗﺘﻠﺔ ﺑﻴﻚ DAKUMA ﺑﻌﺾ ﻗﺘﻠﺔ ﺑﻴﻚ
KHALIFA BNL KAYYAD YA KAWO TA CIKIN TARIKH 1/181.
.
HAKA IBN ASAKIR CIKIN TARIKHU DIMASHQ.
HAKIM CIKIN MUSTADRAK 3/370:
KUMA BATA INGANTABA;
.
* SABODA JAHALAR ﻋﻢ ﻳﺤﻴﻰ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺍﻟﺄﻧﺼﺎﺭﻱ.
.
*SANNAN KUMA JUWAIRIYYA SHI KADAI YARUWAICETA DAGA YAHYA, BAI SAMU MUTA BA'A BA, SANNAN KUMA BA'ASANSHI DA RUWAYA AGURINSABA.
.
* AKWAI IBDIRA BI CIKIN LAFUZZAN RUWAYAR; DON HAKA TA SABAWA SAURAN RUWAYOYINDA KE NUNA MARWAN NE YAKASHE DALHA.
.
** ATAKAICE DAI HUJJOJINNASA BASU INGANTABA.
GAME DA WANDA YA KASHE DALHA MALAMAI SUN KASU GIDA BIYU:
.
1: WADANDA SUKE GANIN BA MARWANNE YAKASHE DALHA BA,
IBN KASIR YAFADA CIKIN BIDAYA 7/248:
ﻭﻗﺪ ﻗﻴﻞ: ﺍﻟﺬﻱ ﺭﻣﺎﻩ ﻏﻴﺮﻩ, ﻭﻫﺬﺍ ﻋﻨﺪﻱ ﻗﺮﺏ, ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﺄﻭﻝ ﻣﺸﻬﻮﺭﺍ.
HAKIKA ANCE BA SHI -MARWAN - BANE YAJEFI DALHA DAMASHINDA YAKASHESHI, KUMA WANNAN RA'AYIN SHINE YAFI KUSA DA DAIDAI AGURINA, KODA DAI MAGANAR FARKO- CEWA MARWANNE YAKASHE DALHAN- TA SHAHARA DAYAWA.
.
2: WADANDA SUKA TAFI KAN CEWA MARWANNE YAKASHE DALHA DIN, SUN KAFA HUJJA DA RUWAYOYI DA BINCIKE YANUNA DAYAN WADANNANNE:
.
* WADANDA SANADIN BAI INGANTABA KAI TSAYE, WANDA KUMA RUWAYOYIN SUN KAI GUDA BIYAR, AMMA DUKA BASU DA INGANCI.
.
** RUWAYOYINDA ISNADINSU KALAU YAKE, SAI DAI ILLAR RUWAYARSU, MARUWAITANSU BASU HALACCI KISSAR BA; DON HAKA YA AKAI KUMA SUKA BADA LABARIN ABUNDA YAFARU AFILIN YAQIN, BAYAN BASU HALACCE SHIBA, BA TARE DA KUMA SUN FADI AGUN WA SUKA JI BA.
.
ATAKAICE DAI KENAN MARWAN BA SHI NE YAKASHE DALHA BA.
.
.
ZAMU CIGABA!!



FITOWA TA )6(.
.
FARKON WANDA ZAI FARA CANJA SUNNAR ANNABI DAGA BANU UMAYYA YAKE??????
.
IBN ABIY ASIM YA FITAR CIKIN AL'AWA'IL 1/77
" ﺃﻭﻝ ﻣﻦ ﻳﻐﻴﺮ ﺳﻨﺘﻲ ﺭﺟﻞ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﻣﻴﺔ".
MUTUMIN FARKO DAZAI FARA CANJA SUNNATA DAGA BANU UMAYYA YAKE.
.
*WANNAN HADISIN YANA DA ILLOLINDA ZASU HANA SHI INGANTA KAMAR YANDA BAYANI ZAIZO, GABA NIN HAKA ZAMU BADA AMSA GA WANNAN NUQDAR:
.
MAL. ALBANI YA KAWO WANNAN HADISIN ACIKIN SILSILAR SAHIHA LAMBA: 1749: YAKUMA HASSANA SHI,
ﻗﻠﺖ ﻭﻫﺬﺍ ﺳﻨﺎﺩ ﺣﺴﻦ.
.
** WANNAN HASSANAWAR DA MAL. ALBANI YAIWA HADISIN YA SHA'AFA NE DA ILLAR DAKE CIKIN HADISIN, SAI YAYI MASA HUKUNCI DA MAZAJEN SANADIN KADAI.
.
ABUNDA ZAI KARA TABBATAR DA HAKAN KUMA SHI NE: MAL. ALBANI AKARKASHIN HADISIN KWATA KWATA BAIYI MAGANAR ILLAR DA ZAMU FADI BA, WANDA HAKAN KE NUNA CEWA BAI LURA DA ITA BANE.KUMA DAMAN MANHAJINMU SHINE : KARBAR MAGANAR MALAMI IDAN TADACE DA ABUNDA BINCIKE YATABBBATAR, DAKUMA RABUWA DA ITA IDAN TASABA.
.
*** GA YANDA ABUN YAKE:
SANADIN HADISIN SHINE:
ﻋﺒﻴﺪ
ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﻌﺎﺫ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺑﻲ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﻮﻑ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮ ﺑﻲ ﻣﺨﻠﺪ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﻌﺎﻟﻴﺔ ﻋﻦ ﺑﻲ ﺫﺭ ﻧﻪ ﻗﺎﻝ ﻟﻴﺰﻳﺪ ﺍﺑﻦ ﺑﻲ ﺳﻔﻴﺎﻥ: ﺳﻤﻌﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ:
1: YA ZO ACIKIN RUWAYAR DA IMAMUL BUKARI YAKAWO CIKIN TARIKH, ABUL ALIYAH YACE:
ﻛﻨﺎ
ﻣﻊ ﺑﻲ ﺫﺭ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﺎﻡ,
SUNA SHAM TARE DA ABU ZARRIN SAI ABU ZARR YAFADAWA YAZID BN ABIY SUFYAN HADISIN.
.
WANDA KUMA TARIHI YA NUNA CEWA ABU ZARR BAIJE SHAM ALOKACIN HALIFANCIN S. UMAR BA, SHI KUMA YAZID DIN AHALIFANCIN S. UMAR YAMUTU, KAMAR YANDA IMAMUL BUKHARI YAFADA, HAKAN SAI YAKE NUNA LALLAI ABU ZARR BAI FADI HADISINBA, TUNDA GASHI INDA AKACE YA FADI HADISIN TA RIHI YA NUNA SAI BAYAN MUTUWAR YAZID DINMA GABA DAYA SANNAN YAJE SHAM.
.
IMAMUL BUKHARI:
ﻟﺎ
ﻧﻌﻠﻢ ﺑﺎ ﺫﺭ ﻗﺪﻡ ﺍﻟﺸﺎﻡ ﺯﻣﻦ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻂﺎﺏ.
ﻗﺎﻝ: ﻭﻗﺪ ﻣﺎﺕ ﻳﺰﻳﺪ ﺑﻦ ﺑﻲ ﺳﻔﻴﺎﻥ ﺯﻣﻦ ﻋﻤﺮ.
DUBA: SIYAR NA ZAHABI 8/254.
D/MU'ASSASAT ARRISALA.
.
2: ABUL A LIYAH BAIJI HADISI BA DAGA ABU ZARRI BA.
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺪﻭﺭﻱ: ﺳﺄﻟﺖ ﺍﺑﻦ ﻣﻌﻴﻦ ﺳﻤﻊ ﺑﻮﺍ ﺍﻟﻌﺎﻟﻴﺔ ﻣﻦ ﺑﻲ ﺫﺭ? ﻗﺎﻝ :ﻟﺎ.
DUBA:
SIYAR NA ZAHABI 8/254.
.
KUMA GA SHI DAI AWANNAN HADISIN YA ZONE TAHANYAR ABUL A LIYA DAGA ABU ZARR, DON HAKA KENAN AKWAI INQIDA I KENAN.
.
3: IBN MA'IN YACE:
INDAI ABUL A LIYAH YAYO RUWAYA DAGA ABU ZARR TO AKWAI ABU MUSLIM TSAKANIN ABUL A LIYA DA ABU ZARR- ABUL A LIYA YANA CIRE ABU MUSLIM KENAN, KUMA SHI KANSA ABU MUSLIM DIN MAJHULINE.
ﻧﻤﺎ ﻳﺮﻭﻱ ﻋﻦ ﺑﻲ ﻣﺴﻠﻢ ﻋﻨﻪ, ﻗﻠﺖ: ﻓﻤﻦ ﺃﺑﻮﺍ ﻣﺴﻠﻢ ﻫﺬ? ﻗﺎﻝ ﻟﺎ ﺩﺭﻱ.
ﺭﺍﺟﻊ: ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﺑﻦ ﻣﻌﻴﻦ.
SANNAN IBN ASAKIR CIKIN TARIKHU DIMASHQ YA KAWO RUWAYAR
ﺑﻮﺍ ﺍﻟﻌﺎﻟﻴﺔ ﻋﻦ ﺑﻲ ﻣﺴﻠﻢ ﻋﻦ ﺑﻲ ﺫﺭ.
WANDA KUMA GA SHI IBN MA'IN YA AMBATA CEWA BAISAN WANE ABU MUSLIM DINBA.
DUBA: TARIKHU DIMASHQ 65/250.
.
*** ATAKAICE DAI:
WANNAN HADISIN BAI INGANTABA.
IMAMUL BUKHARI YA AMBATA CEWA BAI INGANTABA.
IBN KASIR YA AMBATA CEWA AKWAI INQIDA I ACIKINSA, BAI KUMA INGATA BA.
.
DUBA:
ALBIDAYA TA IBN KASIR 8/163.
.
ZAMU CIGABA!!




FITOWA TA )7(
.
DUK GAYYAR SHAM MUNA FIKAINE; SABODA SUN SABAWA UMARNIN ANNABI GAME DA LAZIMTAR S. ALI??
.
wannan nuqda ce da take bukatar bayani gameda shubhohinda sarkin gida yakawo akanta; saboda haka zanyi rubutuka akanta domin rushe wadannan shubhohinda yakawo wadanda yake rudar wadanda ba daliban ilmi ba dasu.
.
1: kamar yanda mun sha na na tawa sabaninda s. ALIYYU ya samu da wasun sahabbai ya faru ne bisa kuskure na ijtihadi da sukayi, kuma s. ALIYYU shine akan daidai a abubbanda suka faru, wannan kuma din itace fahimtar s. ALIYYUN kansa, haka muka gani har litattafan sh'a.wanda hakan kuma yke nuna cewa da ace yana da nassi karara wanda annabi yfada masa cewar dukkan abubuwanda zasu faru na sabanin alokacin halifancinsa shine zai zama mai gaskiya acikin lamurran to da mun samu ya yiwa mabiyansa bayani, amma bamu samu hakanba, wanda kuma bayanan s. ALI game da wadanda yake da sbani dasu yake dada tabbatarda cewa babufa wadannan hadisan da ake da awa .
SHI kuma shugaban kowaye akokarinsa na qudunduno shi'ance a rigar sufanci sai yace ai annabi ya umarci s. ALI yayaqesu, ya kuma fada masa cewa duk abunda zai faru shine da gaskiya; wanda kuma hakan zai rudi wadanda ba su da ido aharkar karatu sudauka cewa son rai ne kawai yasa wadanda suka samu sabani da s. ALI suka samu ba wani abu dabanba.
.
YA FARA DA KAFA HUJJA DA FADINSA:
.
GA HUZAIFA NAN DAKANSA YANA CEWA:
ﺍﻧﻆﺮﻭﺍ ﻟﻰ ﺍﻟﻔﺮﻗﺔ ﺍﻟﺘﻲ ﺗﺪﻋﻮﺍ ﺇﻟﻰ ﻋﻠﻲ ﻓﺎﻟﺰﻣﻮﻫﺎ.
IDAN AN SAMU FITINA HAR TAKAI AHALIN MA'AIKI SUN FITO KASHI BIYU, JAMA'A SUNA DUKAN SASHENSU DA TAKOBI)YAQI( TO KU LALUBA KUGA WACE TAWAGA CE TAKE KIRA ZUWA GA LAMARIN S. ALIYYU KUJE KU LAZIMCE TA.
.
** AMSA GA WANNAN RUWAYA:
.
1: IBN HAJAR YA KAWOTA CIKIN KITABUL FITANI A FAT'HUL BARI babu isnadi.
BAZZAR ya kawota cikin musnad nasa 7/236 lamba ta 2810, musnad din zaidu bn wahab daga huzaifa.
2: SANADIN RUWAYAR SHINE KAMAR HAKA:
ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﺍﻟﻌﺎﻣﺮﻱ, ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻳﺤﻴﻰ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺑﻦ ﺍﻟﻔﺮﺍﺕ ﺍﻟﻘﺰﺍﺯ, ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺑﻮﺍ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﻤﺴﻌﻮﺩﻱ, ﻋﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺣﺮﻳﺚ ﻋﻦ ﻃﺎﺭﻕ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ, ﻋﻦ ﺯﻳﺪ ﺑﻦ ﻭﻫﺐ ﻗﺎﻝ:
WANDA KUMA MAS'UDIY DINNAN DAN SHI'A NE, KUMA YANA DA MUNKARAN HADISAI DAGA ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺣﺮﻳﺚ, KAMAR YANDA ZAHABI YAFADA CIKIN MIZANUL I'ITIDAL 2/457 LAMBA TA 4434:
ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﺍﻟﻤﺴﻌﻮﺩﻱ , ﻣﻦ ﺫﺭﻳﺔ ﺍﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ, ﺷﻴﻌﻲ ﻓﻴﻪ ﻛﻠﺎﻡ, ﺫﻛﺮﻩ ﺍﻟﻌﻘﻴﻠﻲ. ﻭﻟﻪ ﻋﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺣﺮﻳﺚ ﺧﺒﺮ ﻣﻨﻜﺮ.
HAKA WANNAN MAGANAR TAKE A CIKIN LISANUL MIZANI MA 4/520 LAMBA TA 4316.
BA YA GA MATSLA KUMA TA ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺣﺮﻳﺚ KENAN.
.
** HANYA TA BIYU -wadda itace a musnadin bazzar-:
ﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻳﺤﻴﻰ ﺍﻟﻜﻮﻓﻲ, ﻗﺎﻝ ﺧﺒﺮﻧﺎ ﺑﻮﺍ ﻏﺴﺎﻥ ﻗﺎﻝﺧﺒﺮﻧﺎ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﺣﺮﻳﺚ ﻋﻦ ﻃﺎﺭﻕ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ, ﻋﻦ ﺯﻳﺪ ﺑﻦ ﻭﻫﺐ ﻗﺎﻝ:
wadda itama akwai abubban fadi kanta , amma zan taqaita zuwa ga ishara daya cikin matsalolinda hanyar take dashi, kamar yanda nayi asanadinda yagabata.
ﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻳﺤﻴﻰ yana da rauni:
duba:
ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻀﻌﻔﺎﺀ 1/62 LAMBA ta 483,
da:
ﺍﻟﻀﻌﻔﺎﺀ ﻭﺍﻟﻤﺘﺮﻭﻛﻮﻥ 1/253 lamba 45.
zahabi ya kawo cikin mizanul i'itidali 1/162 lamba ta 4316:
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺪﺍﺭﻗﻂﻨﻲ: ﺿﻌﻴﻒ,
ﻗﻠﺖ: ﻫﻮ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻳﺤﻴﻰ ﺑﻦ ﺍﻟﻤﻨﺬﺭ, ﺷﻴﺦ ﻣﻮﺳﻰ ﺑﻦ ﺳﺤﺎﻕ ﻣﻂﻴﻦ. ﻟﻴﺲ ﺑﺸﻰﺀ .
.
DON haka kenan.ba zai yuwu fakewa da wnnan maganarba don anunawa jama' a cewa son raine yasanya su samun sabani da s. ALIYYU.
.
SAI KUMA BATUN CEWA MUTAN SHAM DUKA MUNAFIQAINE, DAKUMA BATUN CEWA ANNABI YACE DUK INDA S. ALI YAJUYA TO QUR'ANI YANA TATE DASHI, WANDA HAKAN KE NUNA WADANDA BA SA TARE DASHI BA SA TARE DA QUR'ANI KAMAR YANDA BAYANI ZAIZO, DAKUMA AMSOSHI GAMEDA RUWAYOYIN DASAURANSU.
.
ZAMU CIGABA!!




FITOWA TA )8(
.
DUK GAYYAR SHAM MUNA FIKAINE; SABODA SUN SABAWA UMARNIN ANNABI GAME DA LAZIMTAR S. ALI??
.
kamar yanda abaya muka ambata cewa batun cewa annabi )s.a.w( yayi umarni dacewa indai fitina ta faru to a lazimci s. ALI, sannan kuma annabi ya nuna cewa s. ALI duk abunda zai faru yana tare da alqur'ani, zantuka ne marasa inganci; domin masu kafa hujja dasu suna qoqarin nuna cewa sauran wadanda suka sabawa s. ALI sun saba masa ne bisa son rai tare da sun san cewa ANNABI yayi umarni da lazimtarsa akowane hali, wanda kuma lamarin ba haka yake ba.
abaya mun ambata cewa sabanin da yafaru tsakanin s. ALI da mu'awiya ko wanne cikin bangarorin biyu ijtihadi yayi ba wai batune nacewa akwai nassi karara daya kebance wani bangare da umarni bisa yaqinba, kamar yanda s. ALI ya ambata dkansa wanda kuma litattafan shi'a suka ruwaito, yace:
Mungani ya kyautu ne muyaqesu bisa ga ra'ayin kanmu.
BATUN kuwa kafa hujja da hadisin
ﻋﻠﻲ ﻣﻊ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻭﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻣﻌﻪ ﻟﺎ ﻳﻔﺘﺮﻗﺎﻥ ﺣﺘﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺤﻮﺽ.
HADISINE maras inganci,yazo cikin majma'uzzawa id 9/134 lamba ta 14767, bayan ya kawo hadisin sai yace:
ﻓﻴﻪ ﺻﺎﻟﺢ ﺍﺑﻦ ﺑﻲ ﺍﻟﺄﺳﻮﺩ ﻭﻫﻮ ﺿﻌﻴﻒ.
IBN ADIYY yace:
ﺣﺪﻳﺜﻪ ﻟﻴﺴﺖ ﺑﺎﻟﻤﺴﺘﻘﻴﻤﺔ
AL kamil 5/103 lamba ta 915.
DUBA : AL mugniy 1/302 lamba ta 2815:
ﺻﺎﻟﺢ ﺑﻦ ﺍﻟﺄﺳﻮﺩ, ﻣﻨﻜﺮ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ.
zahabiy yace:
ﻭﺍﻩ
DUBA: mizan 2/288 lamba ta 3771.
ALBANIY YA raunana hadisin cikin da'iful ja mi'i 1/555 lamba ta 3802.
HAKANAN kafa hujja da hadisin:
ﻛﺎﻥ ﻋﻠﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺤﻖ ﻣﻦ ﺍﺗﺒﻌﻪ ﺍﺗﺒﻊ ﺍﻟﺤﻖ, ﻭﻣﻦ ﺗﺮﻛﻪ ﺗﺮﻙ ﺍﻟﺤﻖ ﻋﻬﺪﺍ ﻣﻌﻬﻮﺩﺍ ﻗﺒﻞ ﻳﻮﻣﻪ ﻫﺬﺍ.
Dabara niy ya kawo shi cikin mu'ujamul kabir, musnadunnisa i, zikru azwajinnabiyyi 23/330.
HAKANAN yazo cikin majma'uzzawa id 9/134 lamba ta14768
yace:
ﻓﻴﻪ ﺳﻌﺪ ﺑﻦ ﺷﻌﻴﺐ ﻟﻢ ﻋﺮﻓﻪ
awani gurin kuma yace:
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻂﺒﺮﺍﻧﻲ ﻭﻓﻴﻪ ﻣﺎﻟﻚ ﺑﻦ ﺟﻌﻮﻧﺔ ﻭﻟﻢ ﻋﺮﻓﻪ.
wanda kuma hadisin cikinsa akwai ruwat din da akwai tacewa kansu,misali:
* YAZO cikin mizanul i'itidal 4/218, zahabi yace:
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻘﻴﻠﻲ: ﻗﺪ ﺭﻭﻯ ﺣﺎﺩﻳﺚ ﺭﺩﻳﺔ ﺑﺎﻃﻠﺔ.
** YAZO cikin almugniy 2/686 lamba ta 6517:
ﻣﻮﺳﻰ
ﺑﻦ ﻗﻴﺲ.
ﺭﻭﻯ ﻋﻨﻪ ﺃﺑﻮﺍ ﻧﻌﻴﻢ ﺍﻟﻔﻀﻞ ﻟﻪ ﻣﻨﺎﻛﻴﺮ.
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻘﻴﻠﻲ : ﻣﻦ ﺍﻟﻐﻠﺎﺓ ﻓﻲ ﺍﻟﺮﻓﺾ.
KODA ya samu tausiq awasu wuraren.
IBNUL jauziy ya jefe shi ma dacewa yana qirqirar hadisan qarya.
IDAN MUKA DUBA ZAMUGA MASU KOKARIN CIN ZARAFIN BAYIN ALLAH BASU SAMUN HUJJA SAI TA HANYAR MAQALEWA IRIN WADANNAN LABARAN MARASA INGANCI, WANDA MU MUNSANI SAHABBAI SUN SIFFANTU DAYIWA ANNABI )S.A.W( BIYAYYA, SANNAN SHI KANSA S. ALIYYU BAI KAFA HUJJA DA IRIN WADANNAN RUWAYOYINBA ALOKACINDA HAKAN YA FARU, WANDA DA ACE SUN TABBATA BABU YANDA ZA AI YACE AI BISA GA RA'AYIN KANSA NE YAYI YAQI DASU.
.
ZAMU CI GABA!!
.
)SHIN ANNABI YA UMARCI S. ALI DA YAYAQI MU'AWIYA TUN YANA DA RAI((
.
AMSAR TA NA RUBUTU NAGABA.




FITOWA TA )9(.
.
MANZON ALLAH )S.A.W( SHINE YA UMARCI S. ALIYYU YAYAQI MU'AWIYA DA DUK WADANDA BASUYI MASA BAI'A BA????
.
wannan da'awar ita monitan ajin kowaye yayi yana mai kafa hujja da fadinsa:
ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ: ﻣﺮ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻋﻠﻴﺎ ﺑﻘﺘﺎﻝ ﺍﻟﻨﺎﻛﺴﻴﻦ ﻭﺍﻟﻘﺎﺳﻂﻴﻦ ﻭﺍﻟﻤﺎﺭﻗﻴﻦ.
AMSA GAME DA WANNAN RIWAYAR.
wannan hadisine da bai ingantaba, ibn asakir ya fitar dashi 12/185, kuma sanadinsa da'ifi ne jiddan, saboda cikinsa akwai:
i: isma'il bn abbad almuzaniy.
Daraqudniy yace: matrukine.
IBN hibban yace:
ﻟﺎ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻟﺎﺣﺘﺠﺎﺝ ﺑﻪ.
¡¡: sharik bn Abdillah, shi kuma sayyi'ul hifz ne.
¡¡¡: ZAKARIYYA bn yahya )al khazzaz(.
SHI kuma ﺻﺪﻭﻕ ﻟﻪ ﻭﻫﺎﻡkamar yanda hafiz yafadi.
WANNAN hadisin an ruwaito shi da lafuzza mabanbanta dakuma hanyoyi daban daban, wanda babu ko guda daya data inganta acikinsu.
* HAITHAMI YA KAWO SHI CIKIN MAJMA'U, KITABUL FITANI, BABUN FI MA KA NA BAINAHUM YAUMA SIFFIN. 7/238, LAMBA TA 12042, 12043,12044,12045,kuma yabayyana illar kowacce cikin hanyoyin kamar yanda yakawo.
** an ruwaito shi da lafazin ﻣﺮﺕ ﺑﻘﺘﺎﻝ ﺍﻟﻨﺎﻛﺜﻴﻦ ﻭﺍﻟﻘﺎﺳﻂﻴﻦ ﻭﺍﻟﻤﺎﺭﻗﻴﻦ. kamar yanda bazzar yakawo a musnad nasa 2/216 lamba ta 604.
isnadin kuma bai ingantaba, saboda matslar hakim bn jubair, shi yasa shi kansa bazzar din yace:
"ﻭﺣﻜﻴﻢ ﻟﻴﺲ ﺑﺎﻟﻘﻮﻱ".
. IBN hibban ya kawo hakim din a al majru hin nasa 1/49,lamba ta 227.
.DUBA tarjamarsa cikin AL mugni 2/505, lamba ta 402, da mizanu 1/583, lamba 161.
** an ruwaito shi da lafazin ﻋﻬﺪ ﺇﻟﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻘﺘﺎﻝ ﺍﻟﻨﺎﻛﺜﻴﻦ....
kamar yanda yake a musnad na bazzar 3/27 lamba ta 774, yakuma ce:
ﻟﻢ ﻧﺴﻤﻌﻪ ﻟﺎ ﻣﻦ ﻋﺒﺎﺩ ﺑﻦ ﻳﻌﻘﻮﺏ.
wanda kuma shi ABBAD din dan shi'a ne daya ruwaito manakir ababin falalar sayyidiy ALI.
IBN hibban ya kawo shi cikin ALMAJRUHIN 2/173,lamba ta 797.
IBN adiy ya kawoshi ckn al kamil 5/559.
DON haka shima bai ingantaba.
*** AN ruwaito shi da lafazin:
ﻣﺮﺑﻘﺘﺎﻝ ﺛﻠﺎﺗﺔ...
wanda kuma hadisine munkari
ACIKIN sanadinsa akwai
¡: ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺑﻦ ﻋﻂﻴﺔ ﺍﻟﻌﻮﻓﻲ.
ABU hatim yace: ﺿﻌﻴﻒ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ .
!!: ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﻋﻂﻴﺔ.
ABU ZUR'A YACE:
ﻟﻴﺲ ﻫﻮ ﺑﺎﻟﻘﻮﻱ.
¡¡¡: ﺳﻌﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺍﻟﻌﻮﻓﻲ
IMAMU AHMAD YACE: ﺟﻬﻤﻲ.
¡¡¡¡: ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺳﻌﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻦ, SHI KUMA ﻟﻴﻦ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ.
DUBA: ﺍﻟﺄﺑﺎﻃﻴﻞ ﻭﺍﻟﻤﻨﺎﻛﻴﺮ 1/395.
*** AN RUWAITO SHI DA LAFAZIN ﺗﻘﺎﺗﻞ ﺍﻟﻨﺎﻛﺜﻴﻦ ﻭﺍﻟﻘﺎﺳﻂﻴﻦ...
WANDA KUMA HADISINE MAUDU I..
AN RAWAITO SHI DA LAFAZIN:
ﺃﻣﺮﻧﺎ ﺑﻘﺘﺎﻝ ﺛﻠﺎﺛﺔ ﻣﻊ ﻋﻠﻲ.
IBN ASAKIR YAFITAR, KUMA HADISINE MAUDU I; SABODA YAZO TAHANYAR ﺍﻟﻤﻌﻠﻰ,shi kuma ya shahara da qirqirar hadisai.
SANNAN akwai ﺷﺮﻳﻚ ﺍﻟﻘﺎﺿﻲ asanadin, shi kuma ﺳﻴﺊ ﺍﻟﺤﻔﻆ ne..
ATAKAICE dai wannan hadisin bai inganta ba takowacce hanya, saboda tsananin raunin hanyoyinsa..
DUBA: AL MUGNIY 2/510.
MAL. ALBANI YAYI BAYANI MAI FADI GAME DA HANYOYIN HADISIN DUKA, DUBA SILSILAR DA'IFA 10/559 ZUWA 566, LAMBA TA 4907.
DON HAKA KAMAR YANDA MUKA FADI ABAYA, ABUNDA YAFARU TSAKANIN S. ALI DA S. MU'AWIYA IJTIHADINE KOWANNENSU YAYI,BA KUMA NASSINE KARARA YA UMARCI S. ALI DAYAQAR MU'AWIYANBA, KAMAR YANDA MAQARYATA KE RIYAWA.
ZAMU CIGABA.




FITOWA TA )10
.
(.MU'AWIYA-BAYAN MULKI YA TABBATA AHANNUNSA- YA CEWA YA'R S. USMAN KADA YASAKE JI TA AMBACI MAHAIFINTA SABODA TA TAMBAYESHI YA BATUN JININ MAHAIFINTA.
.
MU'AWIYA YACE MATA: ﻓﻠﺎ" ﺳﻤﻌﻨﻚ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺫﻛﺮﺕ ﻋﺜﻤﺎﻥ".
wannan da'awar haka monitan kowaye yayita ayunkurinsa na nunawa duniya cewa batun neman jinin S. usman da mu'awiya yake yi qaryane, kwadayin mulkine kawai yasanya yasami sabani da s. ALI.
.
YAKAFA HUJJA DA FADINSA:
.
YAZO CIKIN ALBIDAYAH WANNIHAYA 4/7, SANNAN IBN TAIMIYYAH KANSA YA KAWO RIWAYAR CIKIN MINHAJ NASA 4/408 KUMA RUWAYACE SAHIHIYA.
ﻟﻤﺎ ﻗﺪﻡ ﺣﺎﺟﺎ ﻓﺴﻤﻊ ﺍﻟﺼﻮﺕ ﻓﻲ ﺩﺍﺭ ﻋﺜﻤﺎﻥ: "ﻳﺎ ﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻨﺎﻩ, ﻳﺎ ﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻨﺎﻩ", ﻓﻘﺎﻝ ﻣﺎ ﻫﺬﺍ? ﻗﺎﻟﻮﺑﻨﺖ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﺗﻨﺪﺏ ﻋﺜﻤﺎﻥ, ﻓﺼﺮﻑ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺛﻢ ﺫﻫﺐ ﻟﻴﻬﺎ ﻓﻘﺎﻝ: ﻳﺎ ﺍﺑﻨﺔ ﻋﻢ ﺇﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻗﺪ ﺑﺬﻟﻮﺍ ﻟﻨﺎ ﺍﻟﻂﺎﻋﺔ ﻋﻠﻰ ﻛﺮﻩ, ﻭﺑﺬﻟﻨﺎ ﻟﻬﻢ ﺣﻠﻤﺎ ﻋﻠﻰ ﻏﻴﻆ, ﻓﺈﻥ ﺭﺩﺩﻧﺎ ﺣﻠﻤﻨﺎ ﺭﺩﻭﺍ ﻃﺎﻋﺘﻬﻢ; ﻭﻟﺄﻥ ﺗﻜﻮﻧﻲ ﺑﻨﺖ ﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺧﻴﺮ ﻣﻦ ﺗﻜﻮﻧﻲ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻣﻦ ﻋﺮﺽ ﺍﻟﻨﺎﺱ, ﻓﻠﺎ ﺳﻤﻌﻨﻚ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺫﻛﺮﺕ ﻋﺜﻤﺎﻥ.
.
AMSA GAMEDA WANNAN DA'AWAR TASA.
.
1: kamar yanda yagabata wannan mutumin bashi da hujjoji bisa ga da'awoyinsa sai dayan biyunnan:
¡: ruwayoyi masu rauni wanda duniya tashaida da rauninsu.
¡¡: lanqwasa nusus ingantattu, wanda duk mai ido ababin ilimi yasan qarya ce kurum.
.
Ananma abunda yafaru kenan:
.
2: wannan labarin bai ingantaba ko kusa ko alama,qarya ce kurum aka danganta ta ga sahabi mu'wiya.
.
* ibn kasir ya kawo ta kamar yanda yagabata abaya kamar haka:
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻠﻴﺚ: ﺣﺪﺛﻨﻲ ﻋﻠﻮﺍﻥ ﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ ﺑﻦ ﻛﻴﺴﺎﻥ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﻗﺪﻡ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻭﻝ ﺣﺠﺔ ﺣﺠﻬﺎ ﺑﻌﺪ ﺍﺟﺘﻤﺎﻉ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻋﻠﻴﻪ, ﻓﻠﻘﻴﻪ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻭﺭﺟﺎﻝ ﻣﻦ ﻗﺮﻳﺶ, ﻓﺘﻮﺟﻪ ﻟﻰ ﺩﺍﺭ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﺑﻦ ﻋﻔﺎﻥ, ﻓﻠﻤﺎ ﺩﻧﺎ ﻟﻰ ﺑﺎﺏ ﺍﻟﺪﺍﺭ ﺻﺎﺣﺖ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺑﻨﺖ ﻋﺜﻤﺎﻥ ﻭﻧﺪﺑﺖ ﺑﺎﻫﺎ....
har zuwa qarshenta.
.
KUMA ruwayar bata ingantaba; saboda acikin sanadinta akawai ﻋﻠﻮﺍﻥ ﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ ko kaceﻋﻠﻮﺍﻥ ﺑﻦ ﺩﺍﻭﺩ duka sunansane wanda kuma munkarul hadis ne:
.
ZAHABI yafada cikin mizan 3/108, lamba ta 5763:
ﻋﻠﻮﺍﻥ ﺑﻦ ﺩﻭﺩ ﺍﻟﺒﺠﻠﻲ, ﻣﻮﻟﻰ ﺟﺮﻳﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ, ﻭﻳﻘﺎﻝ : ﻋﻠﻮﺍﻥ ﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ.
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ: ﻋﻠﻮﺍﻥ ﺑﻦ ﺩﺍﻭﺩ- ﻭﻳﻘﺎﻝ ﻋﻠﻮﺍﻥ ﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ-,
ﻣﻨﻜﺮ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ.
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻘﻴﻠﻲ: ﻟﻪ ﺣﺪﻳﺚ ﻟﺎ ﻳﺘﺎﺑﻊ ﻋﻠﻴﻪ, ﻭﻟﺎ ﻳﻌﺮﻑ ﻟﺎ ﺑﻪ.
ﻭﻗﺎﻝ ﺑﻮﺍ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﻳﻮﻧﺲ: ﻣﻨﻜﺮ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ.
duba tarjamar ﻋﻠﻮﺍﻥﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ din acikin: al mugni fiddu'afa i 2/442, lamba ta :4204.
.
*** BATUNSA KUMA NA CEWA IBN TAIMIYYA YA KAWO HADISIN- YA INGANTA SHI- karya ce kawai da rashin tsoron Allah tare da jahiltar musdalahat na malaman hadisi, wanda kuma son rai da qarya ga malamai shine jagoran sarkin gida- kamar yanda hakan zai kara bayyana garemu a rubutu mai zuwa-, babu inda ibn taimiyya ya inganta ruwayar, balma yayi ishara zuwa ga rauninta sdb ya kawota ne da ﺻﻴﻐﺔ
ﺍﻟﺘﻤﺮﻳﺾ wadda kuma sanannan abune kan cewa kawo riwaya da wannan sigar yana nuni zuwa ga rauninta, ga yanda shaikhul islam din yace:
" ﺑﻞ ﺭﻭﻱ ﻋﻨﻪ ﻧﻪ ﻟﻤﺎ ﻗﺪﻡ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﺣﺎﺟﺎ....
" bal RUWIYA anhu annahu lamma qadimal madinata haaajjan....".
wanda kuma kawo riwaya da wannan sigar yana nunine zuwa ga rauninta kamar yanda maluma suka ambata:
.
NAWAWI yafada cikin:
ﺍﻟﻤﺠﻤﻮﻉ
1/63:
" ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﺻﻴﻎ ﺍﻟﺠﺰﻡ ﻣﻮﺿﻮﻋﺔ ﻟﻠﺼﺤﻴﺢ ﺍﻟﺤﺴﻦ, ﻭﺻﻴﻎ ﺍﻟﺘﻤﺮﻳﺾ ﻟﺴﻮﺍﻫﻤﺎ.
kawo riwaya da sigar RUWIYA, ko YURWA DA sauransu ana amfani dashine ga hadisi mai rauni.
.
AL QASIMIY ya naqalto daga nawawi acikin ﻗﻮﺍﻋﺪ ﺍﻟﺘﺤﺪﻳﺚ
1/210::
" ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺿﻌﻴﻔﺎ ﻓﻠﺎ ﻳﻘﻞ ﻗﺎﻝ ﻓﻌﻞ ﻣﺮ ﻧﻬﻰ, ﻭﺷﺒﻪ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺻﻴﻎ ﺍﻟﺠﺰﻡ, ﺑﻞ ﻳﻘﻮﻝ: ﺭﻭﻱ ﻋﻨﻪ ﻛﺬﺍ, ﺟﺎﺀ ﻋﻨﻪ ﻋﻨﻪ ﻛﺬﺍ, ﻳﺮﻭﻯ ﻳﺬﻛﺮ, ﻳﺤﻜﻰ ﻭﻣﺎ ﺷﺒﻬﻪ.
malam nawawi yayi nuni zuwa ga malami yakawo ingantacciyar riwaya da sigar ruwiya ko yurwa da makamansu kuskurene.
.
** sai mu duba muga da wacce sigar ibn taimiyya yakawo riwayar tukunna kafin muyi masa qarya muce ya inganta ruwayar.
.
ALLAH ka azurta mu tsoronka karabamu da son zuciya da qarya.
.
ZAMU cigaba.




FITOWA TA)11
.
(.HA'INCIN ABDUL JABBAR!!
.
kamar yanda muka ambata cewa wannan mutumin rashin tsoron Allahnsa ya kai ya lanqwasawa mutum magana domin tadace da son zuciyarsa don yasami damar sukan mutum da ita, wanda sababin hakan yana komawa zuwa ga dayan biyunnan:
.
1: ko dai bai karanta maganar dakansaba daga cikin littafin mutum kawai ya taqaitane da karanta ta daga litattafan masu tuhumar wannan malamin.
2: ya karanta dakansa amma rashni tsoron Allah yasa yafito yayiwa malamin qage don yasami abunda zai qarfafi da'awarsa.
.
MISALAN WANNAN AIKINNASA.
.
1: fadinsa: IBN TAIMIYYAH YACE: " S. ALIYYU YAFI MU'AWIYA SON YAQIN YAKASANCE SABODA KAWAI YANA SON KASHE MUTANE DA ZUBDA JININSA... yakuma karanto kamar haka: ibn taimiyya yace:
ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﻣﻤﻦ ﺍﺧﺘﺎﺭ ﺍﻟﺤﺮﺏ ﺍﺑﺘﺪﺍﺀ, ﺑﻞ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺷﺪ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺣﺮﺻﺎ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻗﺘﺎﻝ, ﻭﻛﺎﻥ ﻏﻴﺮﻩ ﺣﺮﺹ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻘﺘﺎﻝ ﻣﻨﻪ.
duba: minhaju 4/200.
sai yafassara fadin ibn taimiyya: ﻭﻛﺎﻥ ﻏﻴﺮﻩ ﺣﺮﺹ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻘﺘﺎﻝ ﻣﻨﻪ.
dacewa: ai ibn taimiyyah yana nufin s. ALI yafi mu'awiya son zubda jini, wanda wannan ha incine ko kadan ibn taimiyyah ba ya nufin s. ALI da wannan maganar, idan muka kalli cewar shaikul islam ya ambata cewa s. ALI da mu'awiyan sunfi kowa neman akame hannu gabarin yaqin don kada azubda jini, kuma acikin rundnonin guda biyune aka samu wadanda suke ganin gwanda ayi yaqin wanda kuma ba sa biyayya ga jagororin, kuma sanannen abune cewa idan fitina tataso jagororin tafia sukan kasa kasheta.. ga nassin maganar:
ﻭﺃﻛﺜﺮ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺨﺘﺎﺭﻭﻥ ﺍﻟﻘﺘﺎﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﻂﺎﺋﻔﺘﻴﻦ ﻟﻢ ﻳﻜﻮﻧﻮﺍ ﻳﻂﻴﻌﻮﻥ ﻟﺎ ﻋﻠﻴﺎ ﻭﻟﺎ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ, ﻭﻛﺎﻥ ﻋﻠﻲ ﻭﻋﺎﻭﻳﺔ-ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ- ﺃﻃﻠﺐ ﻟﻜﻒ ﺍﻟﺪﻣﺎﺀ ﻣﻦ ﻛﺜﺮ ﺍﻟﻤﻘﺘﺘﻠﻴﻦ ﻟﻜﻦ ﻏﻠﺒﺎ ﻓﻴﻤﺎ ﻭﻗﻊ. ﻭﺍﻟﻔﺘﻨﺔ ﺫﺍ ﺛﺎﺭﺕ ﻋﺠﺰ ﺍﻟﺤﻜﻤﺎﺀ ﻋﻦ ﺇﻃﻔﺎﺀ ﻧﺎﺭﻫﺎ.
duba: minhajussunnah 4/221.
YANZU wannan idan da tsoron ALLAH taya ya za ace fadinsa
ﻭﻛﺎﻥ ﻏﻴﺮﻩ yana nufin s. ALI indai ba ha inciba da rashin tuna gamuwa da ALLAH??
MISALI na biyu)2(.
FADINSA: tsohon harrana- dan taimiyya- yagama duk tawilin da zaiyi qarshe dakansa yadawo yace yaqar mu'awiya shine adalci, ga abinda yafada acikin minhajul bida ah:
ﻫﺬﺍ ﺩﻟﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﻭﺃﺻﺤﺎﺑﻪ ﺑﻐﺎﺓ, ﻭﺃﻥ ﻗﺘﺎﻝ ﻋﻠﻲ ﻟﻬﻢ ﻗﺘﺎﻝ ﻫﻞ ﺍﻟﻌﺪﻝ ﻟﺄﻫﻞ ﺍﻟﺒﻐﻲ......
WANDA SHIMA NAN IDAN MUKA DUBA RASHIN TSORON ALLAH NE YASA SHI DANGANTAWA IBN TAIMIYYAH WANNAN MAGANAR ALHALIN IBN TAIMIYYA YANA HAKAITO RA'AYIN MALAMAINE GAMEDA HADISIN ﺗﻘﺘﻞ
ﻋﻤﺎﺭﺍ INDA YAKE CEWA:
ﺑﻞ ﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻋﻠﻰ ﺛﻠﺎﺛﺔ ﻗﻮﺍﻝ:
SAI YAFARA AMBATO SU:
ﻓﻂﺎﺋﻔﺔ ﺿﻌﻔﺘﻪ ﻟﻤﺎ ﺭﻭﻱ ﻋﻨﺪﻫﺎ ﺑﺄﺳﺎﻧﻴﺪ ﻟﻴﺴﺖ ﺛﺎﺑﺘﺔ ﻋﻨﺪﻫﻢ.... yacigaba da bayani har zuwa fadinsa:
ﻭﻣﻨﻬﻢ ﻣﻦ ﻗﺎﻝ: ﻫﺬﺍ ﺩﻟﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﻭﺃﺻﺤﺎﺑﻪ ﺑﻐﺎﺓ, ﻭﺃﻥ ﻗﺘﺎﻝ ﻋﻠﻲ ﻟﻬﻢ ﻗﺘﺎﻝ ﻫﻞ ﺍﻟﻌﺪﻝ ﻟﺄﻫﻞ ﺍﻟﺒﻐﻲ ﻟﻜﻨﻬﻢ ﺑﻐﺎﺓ
ﻣﺘﺄﻭﻟﻮﻥ ﻟﺎ ﻳﻜﻔﺮﻭﻥ ﻭﻟﺎ ﻳﻔﺴﻘﻮﻥ.
DUBA: minhajussunnah 4/188.
sai ABDUl jabbar yashafe fadin ibn taimiyyah:
ﻭﻣﻨﻬﻢ ﻣﻦ ﻗﺎﻝ don yasami damar danganta masa maganar kada agane cewa ra'ayin wasu yake hakaitowa, babu abun mamaki ma kuma irin runtse idonsa ga amsar da ibn taimiyya din yabaiwa masu wannan ra'ayin, inda yake cewa:
ﻭﻟﻜﻦ ﻳﻘﺎﻝ: ﻟﻴﺲ ﻓﻲ ﻣﺠﺮﺩ ﻛﻮﻧﻬﻢ ﺑﻐﺎﺓ ﻣﺎ ﻳﻮﺟﺐ ﺍﻟﺄﻣﺮ ﺑﻘﺘﺎﻟﻬﻢ......
DON ganewa idonka yanda lamarin yake dakuma ha incin da sarki yatafka sai kakoma minhaju 4/189.
.
AMMA babu kunya sai yarufe idonsa yahsafe abunda zai shafe don yasamarwa qaryarsa dalili.
.
MISALI na uku)3(.
fadinsa: ibn taimiyyah yace:
ﺛﻢ ﻋﻠﻴﺎ ﺑﺪﺃﻫﻢ ﺑﺎﻟﻘﺘﺎ) s. ALI ne yafara yaqar mu'awiya(.
anama sarkin ya sake tafka ha incin dayasaba domin shaikhul islam hakaito ra'ayin wasu yake yi agabar inda yace:
ﻭﺃﻣﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ- ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ - ﻛﺎﻥ ﻣﺼﻴﺒﺎ ﻓﻲ ﻗﺘﺎﻟﻪ ﻟﻪ, ﻭﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻋﻠﻲ- ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ-ﻣﺼﻴﺒﺎ ﻓﻲ ﻗﺘﺎﻟﻪ ﻟﻤﻌﺎﻭﻳﺔ ﻓﻘﻮﻟﻬﻢ ﺃﺿﻌﻒ ﻣﻦ ﻗﻮﻝ ﻫﺆﻟﺎﺀ....
yacigaba da kawo dalilin masu wannan ra'ayin:
ﺛﻢ ﺇﻥ ﻋﻠﻴﺎ ﺑﺪﺃﻫﻢ ﺑﺎﻟﻘﺘﺎﻝ ﻓﻘﺎﺗﻠﻮﻩ ﺩﻓﺎﻋﺎ ﻋﻦ ﻧﻔﺴﻬﻢ ﻭﺑﻠﺎﺩﻫﻢ.
ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﻭﻛﺎﻥ ﻋﻠﻲ ﺑﺎﻏﻴﺎ ﻋﻠﻴﻬﻢ.
duba: minhaju 4/405.
AMMA duk dahaka sai yarintse ido yadangantawa ibn taimiyyah wannan ra'ayin, babu kuma abun mamaki irin idan kaga ibn taimiyyan kansa yayiwa masu wannan ra'ayin raddi dafadinsa:
ﻭﺃﻣﺎ ﻗﻮﻝ ﺍﻟﻘﺎﺋﻞ: ﺇﻥ ﻋﻠﻴﺎ ﺑﺪﺃﻫﻢ ﺑﺎﻟﻘﺘﺎﻝ.
ﻗﻴﻞ ﻟﻪ: ﻭﻫﻢ ﻭﻟﺎ ﺍﻣﺘﻨﻌﻮﺍ ﻣﻦ ﻃﺎﻋﺘﻪ ﻭﻣﺒﺎﻳﻌﺘﻪ ﻭﺟﻌﻠﻮﻩ ﻇﺎﻟﻤﺎ ﻣﺸﺎﺭﻛﺎ ﻓﻲ ﺩﻡ ﻋﺜﻤﺎﻥ, ﻭﻗﺒﻠﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﺷﻬﺎﺩﺓ ﺍﻟﺰﻭﺭ, ﻭﻧﺴﺒﻮﻩ ﻟﻰ ﻣﺎ ﻫﻮ ﺑﺮﻱ ﻣﻨﻪ....
Don ganewa idonka koma minhaju 4/411.
WANDA wannan ba ya hakaito komai illa ha inci da rashin tsoron ALLAH ababin naqali.
.
BANDA kuma karyar da yayiwa ibn taimiyya kan cewa ya soki hadisin ﺗﻘﺘﻞ ﻋﻤﺎﺭﺍ wai yace ba mutawatiri bane... wanda itama wannan qaryar idan hali yayi zamu warwareta insha allah.
.
ZAMU cigaba!!




FITOWA TA )12
.
(.HINDU) MAHAIFIYAR MU'AWIYA( ITA TASANYA WAHASHI YAKASHE HAMZA, BAYAN KUMA AN KASHE HAMZAN SAI TA TAUNA HANTARSA.
.
MONITA YACE: " mai cin hanta danya, ai ta bari dai adafa ko".
.
WANNAN MAGANAR TASA MAGANA CE DA TAKE SHAHARARRIYA AWANNAN ZAMANIN NAMU MUSAMMAN GUn WADANDA SUKE KOYAR TARIHI DAGA FILM DIN THE MESSAGE, BAI KUMA DACE ACE TA FITO DAGA BAKIN SARKIN BAHASI KAMAR ABDUL JABBAR BA, INDAI KUMA BA KARYAR BAHASIN AKEYIBA.
.
DON BADA AMSAR WANNAN MAGANAR TASA NAKE CEWA:
.
* yana da kyau muzo da wasu ya'n tambayoyi wadanda keda alaqa da wannan tatsuniyar saboda zasu taimaka mana mufahimci lamarin yanda yake, tambayoyin kwa sune:
.
1:WANENE YAKASHE S. HAMZA?
2: ME YASA YAKASHESHI?? GASKIYANE CEWA HINDU CE TASA YAKASHE SHI DIN???
3: SHIN YA INGANTA CEWA HINDU TA TAUNA HANTAR S. HAMZA BAYAN TA SA AN FARKE CIKINSA????
4: SHIN AN SAMU ATARIHI WANI CIKIN SAHABA YA KIRATA DA " MAI CIN HANTA"??
5: MENENE HUKUNCIN WANDA YA AIKATA LAIFI ALOKACIN JAHILIYYA SAI KUMA YADAWO YA MUSULUNTA ??.
.
**** AMSAR TAMBAYA TA 1:
wanda yakashe s. HAMZA shine:
wahshiyyu bn harb, abu nu'aim ya kawo cikin ﻣﻌﺮﻓﺔ
ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ:
ﻭﺣﺸﻲ ﺑﻦ ﺣﺮﺏ ﺍﻟﺤﺒﺸﻲ ﺑﻮﺍ ﺩﺳﻤﺔ ﻣﻮﻟﻰ ﺟﺒﻴﺮ ﺑﻦ ﻣﻂﻌﻢ ﺑﻦ ﻋﺪﻱ ﺑﻦ ﻧﻮﻓﻞ, ﻗﺎﺗﻞ ﺣﻤﺰﺓ.
wanda kuma ya dawo daga baya ya musulunta tun annabi yana raye, sannan shine yakashe musailimah- wanda yayi da'awar annabta-.
IBN kasir yace:
ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺴﻴﻠﻤﺔ ﻓﻌﻘﺮﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻳﺪﻱ ﻭﺣﺸﻲ ﺑﻦ ﺣﺮﺏ.
AL BIDAYA 6/375.
.
AMSA TABIYU:
sam sam ba hinduce tasanya WAHSHI yakashe s. HAMZA ba kamar yanda yayadu abakunan mutane, bal JUBAIR BN MUD'IM shine yasanya shi yakashe S. HAMZAN amatsayin daukar masa fansar baffansa da s. HAMZA yakashe.
IMAMUL BUKHARI YA KAWO CIKIN SAHIH NASA:
ﺑﺎﺏ ﻗﺘﻞ ﺣﻤﺰﺓ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻤﻂﻠﺐ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ
5/100.
YAKAWO ISNADI HAR ZUWA AMRU BN UMAYYAH ADDUMARIY YACE;
ﺧﺮﺟﺖ ﻣﻊ ﻋﺒﻴﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺪﻱ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻴﺎﺭ, ﻓﻠﻤﺎ ﻗﺪﻣﻨﺎ ﺣﻤﺺ, ﻓﻠﻤﺎ ﻗﺪﻣﻨﺎ ﺣﻤﺺ ﻗﺎﻝ ﻟﻲ ﻋﺒﻴﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺪﻱ: ﻫﻞ ﻟﻚ ﻓﻲ ﻭﺣﺸﻲ ﻧﺴﺄﻟﻪ ﻋﻦ ﻗﺘﻞ ﺣﻤﺰﺓ, ﻗﺎﻝ: ﻧﻌﻢ.
ACIKIN HADISIN DAI SAI YACE:
ﻓﻜﺸﻒ ﻋﺒﻴﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﻭﺟﻬﻪ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﻟﺎ ﺗﺨﺒﺮﻧﺎ ﺑﻘﺘﻞ ﺣﻤﺰﺓ? ﻗﺎﻝ ﻧﻌﻢ: ﺣﻤﺰﺓ ﻗﺘﻞ ﻃﻌﻴﻤﺔ ﺑﻦ ﻋﺪﻱ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻴﺎﺭ ﺑﺒﺪﺭ, ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻲ ﻣﻮﻟﺎﻱ ﺟﺒﻴﺮ ﺑﻦ ﻣﻂﻌﻢ: ﻗﺘﻠﺖ ﺣﻤﺰﺓ ﺑﻌﻤﻲ ﻓﺄﻧﺖ ﺣﺮ.
UBAIDULLAHI YA TAMBAYI WAHSHI YABASU LABARIN KASHE HAMZA SAI YACE MUSU:

" hakika hamza ya kashe du'aima bn addiyyi a badar, sai JUBAIR BN MUD'IM yace mini idan kakashe hamza kadaukar min fansar jinin baffana to na ya'nta ka.
IBN hibban ma ya kawo ruwayar cikin sahih nasa 15/484.
.
DON HAKA BATUN MA ACE HINDUCE TASA WAHASHIN YAI KISAN BA DAI DAI BANE, TUNDA GA ABUNDA INGANTACCIYAR RUWAYA TANUNA.
.
** ME YASA TO WAHASHIN YAI KISAN??
.
kamar yanda ruwaya tanuna cewa uban gidan wahshi dinne yanemi yakashe hamzan indai yayi hakan to zai ya'n ta shi, shi yasa shi kuma kwadayin samun ya'nci yasanya shi yin hakan, kamar yanda ruwaya tanuna, wahshin yace:
ﺪﺧﻠﺖ ﺍﻟﻤﻌﺮﻛﺔ-ﺣﺪﺍ- ﻭﻟﺎ ﺭﻳﺪ ﺍﻟﻘﺘﺎﻝ ﻟﺎ ﺭﻳﺪ ﺣﻤﺰﺓ ﻟﺄﻛﻮﻥ ﺣﺮﺍ.
YANZU DAI ANAN MUN GAMA DA BATUN CEWA HINDU CE TASA AKA KASHE HAMZA, MUNJI YANDA ABUN YAFARU.
.
AMSAR TAMBAYA TA UKU:

BAI TABBATA TA INGANTACCIYAR RUWAYA CEWA HINDU TA SA AN FARKE CIKIN HAMZA HAR TA TATTAUNA HANTARSABA, WANNAN TATSUNIYA CE KURUM, BYANI FILLA FILLA GAMEDA RASHIN INGANCIN RUWAYOYIN DASUKA ZO DA WANNAN TATSUNIYAR ZAI ZO ARUBUTU NAGABA.
ZAMU CIGABA!!




FITOWA TA )13
.
(.CI GABA!!
.
HINDU TA SA AN CIRO MATA HANTAR S. HAMZA TA TAUNA TA BAYAN TA SANYA AN FARKE CIKINSA!!???
Kamar yanda arubutunda yagabata abaya mun isha ra zuwa ga bacin ruwayar dake nuna haka, ga yanda lamarin yake:
* imamu Ahmad ya kawo ta kamar haka4/44:
" ﻓﻨﻆﺮﻭﺍ ﻓﺈﺫﺍ ﺣﻤﺰﺓ ﻗﺪ ﺑﻘﺮ ﺑﻂﻨﻪ, ﻭﺃﺧﺬﺕ ﻫﻨﺪ ﻛﺒﺪﻩ ﻓﻠﺎﻛﺘﻬﺎ ﻓﻠﻢ ﺗﺴﺘﻂﻊ ﺗﺄﻛﻠﻬﺎ.
ISNADINTA shine:
ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﻔﺎﻥ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺣﻤﺎﺩ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﻂﺎﺀ ﺑﻦ ﺍﻟﺴﺎﺋﺐ ﻋﻦ ﺍﻟﺸﻌﺒﻲ.
ILLOLIN WANNAN RUWAYAR.
* ADA'U BN ASSA'IB: ya sami ikhtiladi.
DUBA tarjamarsa cikin ﺍﻟﻀﻌﻔﺎﺀ ﻭﺍﻟﻤﺘﺮﻭﻛﻮﻥ 2/17
LAMBA 2307.
imam AHMAD yace:
ﻣﻦ
ﺳﻤﻊ ﻣﻨﻪ ﻗﺪﻳﻤﺎ ﻓﻬﻮ ﺻﺤﻴﺢ ﻭﻣﻦ ﺳﻤﻊ ﻣﻨﻪ ﺣﺪﻳﺜﺎ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﺑﺸﺊ.
duba: al kamil 7/73.
** HAMMAD: yaji daya ADA'U dinne bayan ikhtilad kamar yanda ukailiy yafadi, duba tahzibuttahzib 7/206.
Wasu malaman sukace : hammad yaji daga ADA'U kafin ada'u din yasami ikhtiladi dakuma bayan ikhtiladin, kamar yanda yake a tahzibul kamal.
DON haka ba a sami tantacewa gameda ruwayar nanba shin kafin ikhtiladin yaji ko bayansa, wanda ko wannan kadai ya isa yarushe ruwayar.
** SHA'ABI BAIYI RUWAYA DAGA IBN MAS'UD SABANIN YANDA SANADIN YANUNA.
DUBA :AL MARASIL NA IBN ABI HATIM 1/160 LAMBA 591:
ﺳﻤﻌﺖ ﺑﻲ ﻳﻘﻮﻝ: ﻟﻢ ﻳﺴﻤﻊ ﺍﻟﺸﻌﺒﻲ ﻣﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ.
ATAKAICE DAI RUWAYAR TANA DA TARIN ILLOLI.
## IBN KASIR YA NAQALTO LABARIN A ALBIYAH 4/42 DAGA IBN IS'HAQ ACIKI YAKE CEWA:
ﻭﺑﻘﺮﺕ ﻋﻦ ﻛﺒﺪ ﺣﻤﺰﺓ ﻓﻠﺎﻛﺘﻬﺎ, ﻓﻠﻢ ﺗﺴﺘﻂﻊ ﺗﺴﻴﻐﻬﺎ ﻓﻠﻔﻆﺘﻬﺎ.
WANNAN RUWAYAR MURSALA CE; SABODA IBN ISHAQ DIN YACE ACIKIN SIRA 333: ﻛﻤﺎ ﺣﺪﺛﻨﻲ ﺻﺎﻟﺢ ﺑﻦ ﻛﻴﺴﺎﻥ.
shi kuma salihu bn kaisan yana cikin sigarutta bi'ina, bal baima hadu da sahabbai dayawa ba.
IBN hajar yace:
ﺭﺃﻯ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻭﺍﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ.
tahzibuttahzib 4/399 lamba 692.
SHI kuma hadisi mursal da'ifine.
IMAMU muslim yace:
ﻭﺍﻟﻤﺮﺳﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﻭﺍﻳﺎﺕ ﻓﻲ ﺻﻞ ﻗﻮﻟﻨﺎ ﻭﻗﻮﻝ ﻫﻞ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺑﺎﻟﺄﺧﺒﺎﺭ ﻟﻴﺲ ﺑﺤﺠﺔ.
### al waqidiy ya kawo ta da laazin:
ﻋﻦ
ﻭﺣﺸﻲ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ: ﻓﺸﻘﻘﺖ ﺑﻂﻨﻪ ﻓﺄﺧﺮﺟﺖ ﻛﺒﺪﻩ, ﻓﺠﺌﺖ ﺑﻬﺎ ﺇﻟﻰ ﻫﻨﺪ ﺑﻨﺖ ﻋﺘﺒﺔ ﻓﻘﻠﺖ: ﻣﺎﺫﺍ ﻟﻲ ﻗﺘﻠﺖ ﻗﺎﺗﻞ ﺑﻴﻚ
acikin ruwayar yace:
ﻓﻤﻀﻐﺘﻬﺎ ﺛﻢ ﻟﻔﻆﺘﻬ.
SHI kuwa waqidiy matrukine.
BUKHARI YACE: ﻣﺘﺮﻭﻙ, DUBA: ﺍﻟﻀﻌﻔﺎﺀ ﺍﻟﺼﻐﻴﺮ 1/123,
lamba ta 350.
wasu malamnma sunce yana qirqirar hadisai na karya , kamar yanda imamu AHMAD da is'haq suka fadi, duba tahzib 9/426.
DUBA tarjamarsa cikin addu'afa u wal matru kun na imam annasa iy 1/92 lamba ta 531.. da addu'afa u na daraqudniy 3/130 lamba ta 477.
DON HAKA RUWAYARSA BATA INGANTABA.
#### an rawaito cewa tayi alkawarin sai ta tauna hantarsane sakamakon kashe mata mahaifi dayayi, kamar yanda baihaqi yakawo cikin dala il 3/282 acikin kissar yake cewa:
ﻭﺍﺣﺘﻤﻠﺖ
ﻛﺒﺪﻩ, ﺣﻤﻠﻬﺎ ﻭﺣﺸﻲ ﻭﻫﻮ ﻗﺘﻠﻪ ﻭﺷﻖ ﺑﻂﻨﻪ, ﻓﺬﻫﺐ ﺑﻜﺒﺪﻩ ﻟﻰ ﻫﻨﺪ ﺑﻨﺖ ﻋﺘﺒﺔ ﻓﻲ ﻧﺬﺭ ﻧﺬﺭﺗﻪ ﺣﻴﻦ ﻗﺘﻞ ﺑﺎﻫﺎ ﻳﻮﻡ ﺑﺪﺭ.
sanadin labarib shine kamar haka:
ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺧﺎﻟﺪ, ﻗﺎﻝ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺑﻲ ﻗﺎﻝ: ﺛﻨﺎ ﺍﺑﻦ ﻟﻬﻴﻌﺔ, ﻋﻦ ﺑﻲ ﺍﻟﺄﺳﻮﺩ ﻋﻦ ﻋﺮﻭﺓ ﺑﻦ ﺍﻟﺰﺑﻴﺮ.
WANDA kuma ibn lahi'ah ya sami ikhtiladi kamar yanda imamul bukhari ya kawo shi cikin littafin addu'afa u assagiru.
SHI kuma muhammad bn amru bn khalid ba'a sami magana akansaba ta jarhi ko ta'adili, wanda wannan kansa ruwaya tazama maras inganci kamar yanda yake sananne agun maluma.
* ibn kasir ya kawo cewa hindu tayi alkawarin sai ta tauna hantar hamza..al bidya 3/334.
amma kuma bai kawo isnadin maganarba.. don haka ba batun inganci; saboda kawo isnadi shine mafita a irin wannan babin.
IMAMU muslim ya kawo a muqaddima:
ﻟﻤﺎ ﻭﻗﻌﺖ ﺍﻟﻔﺘﻨﺔ ﻗﺎﻟﻮﺍ ﺳﻤﻮﺍ ﻟﻨﺎ ﺭﺟﺎﻟﻜﻢ.
muma anan muna neman sanadin.
** ya kawo ta kuma da lafazin:
ﻭﺫﻛﺮ ﻣﻮﺳﻰ ﺑﻦ ﻋﻘﺒﺔ: ﺍﻟﺬﻱ ﺑﻘﺮ ﻋﻦ ﻛﺒﺪ ﺣﻤﺰﺓ ﻭﺣﺸﻲ ﻓﺤﻤﻠﻬﺎ ﻟﻰ ﻫﻨﺪ ﻓﻠﺎﻛﺘﻬﺎ, ﻓﻠﻢ ﺗﺴﺘﻂﻊ ﺗﺴﻴﻐﻬﺎ.
AL bidaya 4/42.
ita kuma wannan akwai irsali acikinta, kuma mun kawo magana kan hadisi mursali; saboda MUSA BN UQBAH YANA DAGA SIGARUT TA BI'IN.
DON haka itama kamar ya'n uwantane.
** dabari ya kawota cikin tarikh 3/61 itama akwai irsali saboda ta tsaya ne akan qatada.
ATAQAICE dai wannan labarin bai ingantaba ko kusa ko alama.
NUQDA tagaba: shin gaskiya ne wasu cikin sahabbai sun cewa mu'awiya: dan mai cin hanta??
tabbas babu inda hakan yatabbta, bayani kuma zai zo arubutu mai zuwa.
.
ZAMU cigaba!!




FITOWA TA )14
.
(.HINDU TA TAUNA HANTAR S. HAMZA.
.
KARKAREWA!
.
KAMAR YANDA ABAYA MUN KAWO CEWA BA HINDU BACE TASANYA AKASHE S. HAMZA, SANNAN MUN DUBA KUMA WASU CIKIN MAGANGANUNDA KE NUNA CEWA BAYAN AN KASHE S. HAMZA TA TAUNA HANTARSA DANYA , WANDA KUMA MUNYI BAYANIN ILLOLIN HANYOYIN DA RASHIN TABBATARSU.
.
ABUNDA YARAGE SHINE:
.
SHIN YA TABBATA CEWA WASU CIKIN SAHABBAI SUN AMBACI HINDU DA MAICIN HANTA??
.
AMSAR ITACE: BABU RUWAYA INGANTACCIYA DATA NUNA HAKAN, YO TO MUN CE MA ITA KANTA KISSAR CIN HANTARMA BATA INGANTABA TO INA BATUN KUMA AMBATONTA DAHAKAN??
.
INGANTACCEN TARIHI BAI TABBATAR DA HAKANBA.
.
YANA dakyau aja hankalin mutane akan karbar tarihi kai tsaye daga fina finai da akeyi natarihi kamar THE MESSAGE wanda ya taimaka wajen yaduwar wannan tatsuniyar atsakanin al'umarmu, musammanma dayazama gidajen talabijin suna watsa shi aduk ranar idi bayan sakkowa daga idi, wanda wannan yasanya yara da manya suka riqe tarihi asalonda film din yake hakaito musu, alhalin shi wannan film din cike yake da labarai marasa inganci, misali:
.
1: qissar saqar gizo gizo alokacin hijirar manzon ALLAH zuwa madina.
2: abunda yasanya hamza yamusulunta saboda ABU jahal ya ya cutar da manzon ALLAH ya zage shi ya aibanta shi, qarshe dai shi kuma hamza dayaji labarin sai yafusata, yaje yadaki ABU jahal din.. har zuwa dai karshen labarin.
ITAMA wannan bata ingantaba, amma kuma ita aka watsa acikin film din.
3: ABU DALIB Ya rasune yana kiran ABU sufyan zuwa ga su sassautawa musulunci su amsa kira mana.
4: an taru ana kida ana rawa ana shan giya sai hindu tafito tabaiwa wahshi kwangilar kashe hamza, har yayi gwaji alokacin.
Itama wannan tatsuniya ce kurum..
WANDA wannan ya sabawa ingantaccen tarihi.
DASAURAN wadannan kusa kurai dake cikin film din.
NAGA wani dan uwa da yataba rubutu akan mukhalafat da marwiyyat dinda basu tabbataba acikin wannan film din- idan na sami yalwar lokaci zan bibiyi abubbanda yafada don tabbatar dasu daga film ko don fadakar da jama'a akai- wanda sukai musharaka cikin samarda film din harda ba'amirike wanda yaje misra yasauka kusan shekara guda.
.
Acikin wadanda suka samarda film din dai babbansu shine: musdafal aqqad, wanda shima ba'amirikene haifaffen siriya, wanda yayi karatu aqasar amrika, daga baya yasami damar fitarda shi wannan film din.
.
SHIN ZAMU DINGA KARBAR TATIHIN ADDININMU NE DAGA GURIN WADANNAN ARNAN MASU YUNQURIN GURBATA ADDININE KO KUMA ZAMUBI INGATTACCEN TARIHI MUDINGA GINA HUKUNCI AKANSANE?
.
wani dan uwa yake fada mini- amma ban sami damar bi dakaina ba yazuwa yanzunnan- farkon film din sun fara ne da ambaton bayan shekara....... da mutuwar annabi isa...
WANDA kuma wannan ya sabawa abunda al qur'ani yatabbatar:
"ﻭﻣﺎ ﻗﺘﻠﻮﻩ ﻭﻣﺎ ﺻﻠﺒﻮﻩ ﻭﻟﻜﻦ ﺷﺒﻪ ﻟﻬﻢ".
YA zama dole mutantance ingantaccen tarihi daga gurbataccensa tahanyar bibiyar hanyoyinda yazo.
KUMA mudauka ma ya tabbata cewa ya tabbata hindu din ta ci hantar, shin ba ta dawo ta musuluntaba? SHIN ba ance:
"ﻳﻨﺘﻬﻮﺍ ﻳﻐﻔﺮ ﻟﻬﻢ ﻣﺎ ﻗﺪ ﺳﻠﻒ"?
ko bai tabbata ba cewa:
"ﺍﻟﺈﺳﻠﺎﻡ ﻳﺠﺐ ﻣﺎ ﻗﺒﻠﻪ".
SHIN daman ya halatta a aibantawa mutum da abunda ya aikata kafin musuluntarsa?? BALLANTAna kuma abunda bai tabbata ba.
.
AKARSHE ina jan hankalin ya'n uwa daluban ilimi dasu nema littafi mai sunan:
ﻣﺎ ﺷﺎﻉ ﻭﻟﻢ ﻳﺜﺒﺖ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻴﺮﺓ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ.
wanda aciki ya kawo abubuwa dadama na tarihi wanda sun yadu amma kuma basu tabbataba, ya kuma yi bayani zuwa ga bacinsu.
hatta ita kanta wannan tatsuniyar ta kisan s. HAMZA ya kawota ashafin 147-152.
.
SHIMA mal. ALBANI acikin fiqhus sirah 279-280, yadanyi bayani akan mas'alar.
ZAMU taqaita anan murufe wannan shafin don tsallakawa zuwa nuqda ta gaba:
.
zamu cigaba




FITOWA TA )15
.
(.UMMUNA AISHA R.A TA KWATANTA MULKIN MU'AWIYA R. DA MULKIN MU'AWIYA.
.
sarkin kuri yace:
.
''zamu basu amsa da abunda sayyidatuna AISHA ta fada gameda tsayin mulkin mu'awiyan, ga abunda tace:
ﻗﺪ ﻣﻠﻚ ﻓﺮﻋﻮﻥ ﻣﺼﺮ ﺃﺭﺑﻌﻤﺎﺋﺔ ﺳﻨﺔ.
ai fir'auna ma yayi mulkin masar tsawon shekara 400...
.
AMSA GAMEDA WANNAN RUWAYAR DA YAQUDUNDUNO A ALJIHUNSA.
.
1: Wannan labarin ibn asakir ya kawo shi cikin tarikhu dimashq 59/145.
hakanan zahabiy ya kawo shi cikin siyar 3/143.
Dasanadi kamar haka:
ﺃﻳﻮﺏ ﺑﻦ ﺟﺎﺑﺮ: ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺇﺳﺤﺎﻕ, ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺄﺳﻮﺩ:
ﻗﻠﺖ ﻟﻌﺎﺋﺸﺔ:....
** lafazinta kuma shine:
"ﺃﻟﺎ ﺗﻌﺠﺒﻴﻦ ﻟﺮﺟﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻂﻠﻘﺎﺀ ﻳﻨﺎﺯﻉ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﺎﻟﺨﻠﺎﻓﺔ? ﻗﺎﻟﺖ: ﻭﻣﺎ ﻳﻌﺠﺐ? ﻫﻮ ﺳﻠﻂﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺆﺗﻴﻪ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﻔﺎﺟﺮ, ﻭﻗﺪ ﻣﻠﻚ ﻓﺮﻋﻮﻥ ﻣﺼﺮ ﺃﺭﺑﻌﻤﺎﺋﺔ ﺳﻨﺔ.
## alafazin da ibn kasir yakawo a al bidaya 8/140 ya kawo ta da karin lafazin:
ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ.
wanda kuma shima ya kawotane da wannan isnadin, inda yace:
ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﻋﺴﺎﻛﺮ ﺑﺈﺳﻨﺎﺩﻩ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﺍﻟﻂﻴﺎﻟﺴﻲ: ﺛﻨﺎ ﺃﻳﻮﺏ ﺑﻦ ﺟﺎﺑﺮ....
2: wannan ruwaya bata tabbataba saboda illoli kamar haka:
ILLA ta farko:
* AYYUB BN JABIR dayazo a isnadin, wanda shi kuma da'ifine, bal ibnil madini ma yace :
ﻳﻀﻊ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ.
duba: mizanu 1/285.
NASA'I yace: ﺿﻌﻴﻒ.
addu'afa u wal matrukun 1/16 lamba 25.
IBN hibban yace:
ﻳﺨﻂﺊ ﺣﺘﻰ ﺧﺮﺝ ﻋﻦ ﺣﺪ ﺍﻟﺈﺣﺘﺠﺎﺝ ﺑﻪ ﻟﻜﺜﺮﺓ ﻭﻫﻤﻪ.
al majruhin 1/168, lamba :96.
IBN ma'in ya da'aafa shi.
DUBA: al kamil fi du'afa irrijal 2/17 lamba 184.
ABU zur'a yace:
ﻭﺍﻫﻲ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ.
aljarhu watta'adil 2/243,lamba 862.
ILLA TA BIYU:
AN'ANA TA ABU IS'HAQ - kamar yanda yake a isnadin: ﺃﺑﻲ ﺇﺳﺤﺎﻕ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺄﺳﻮﺩ- WANDA SHI KUMA ABU IS'HAQA YANA YIN TADLISI.
SALAHUDDINIL ala'iy yake fadi akan ABU is'haq acikin jami'ut tahsil 1/245 lamba 576:
ﺗﻘﺪﻡ ﺃﻧﻪ ﻣﻜﺜﺮ ﺍﻟﺘﺪﻟﻴﺲ..
ibn hajar ya kawo shi cikin : ta'arifu ahlittaqdis a dabaqa ta uku lamba ta 91, inda yace:
ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺴﺒﻴﻌﻲ ﺍﻟﻜﻮﻓﻲ, ﻣﺸﻬﻮﺭ ﺑﺎﻟﺘﺪﻟﻴﺲ.
wanda kuma awannan hadisi bai sarraha sama'iba, kuma ibn hajar ya fadi cewa ya'n dabaqa ta uku sune:
ﻣﻦ ﻛﺜﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﺪﻟﻴﺲ ﻓﻠﻢ ﻳﺤﺘﺞ ﺍﻟﺄﺋﻤﺔ ﻣﻦ ﺃﺣﺎﺩﻳﺜﻬﻢﻟﺎ ﺑﻤﺎ ﺻﺮﺣﻮﺍ ﺑﺎﻟﺴﻤﺎﻉ.
p 14.
WANNAN illolinda suka sanya sanadin hadisin yazama mai rauni kenan.
.
ATAQAICE dai: wannan tatsuniyace kurum amma bai tabbata nana Aisha ta fadeshiba.
.
SANNAN matanin hadisin kansa akwai nakara cikinsa tunda akwai sahihan hadisai dake nuna kyawun alaqarda ke tsakanin ummuna da s. MU'AWIYA, ga abunda take cewa:
"ﺇﻧﻲ
ﻟﺄﺗﻤﻨﻰ ﻳﺰﻳﺪ ﺍﻟﻠﻪ -ﻋﺰ ﻭﺟﻞ- ﻣﻦ ﻋﻤﺮﻱ ﻓﻲ ﻋﻤﺮﻩ.
addabaqat 41..
baya kuma da makamantan irin wadannan da aka rawaito daga gareta wanda idan hali yayi zamu bayyana su.
.
ZAMU CGB!!




FITOWA TA )16 (.BANU UMAYYATA BISAFITIN AMMAH MUTANEN BANZANE, BA'AYI MUTUMIN KIRKI ACIKINSU BA.)
sayyadi Ali yazo don yagyara kujerar annabi da yatarar an bata ta ta sakwarkwaci.
.
(.SARKI yakafa dalili yana maicewa:
.
tirmizi dayake yafi abu dawuda dama dama shi ya dake ya kawo ruwaya, sa'id bn jahman yace:
ﻛﺬﺏ ﺑﻨﻮﺍ ﺍﻟﺰﺭﻗﺎﺀ ﺑﻞ ﻫﻢ ﺷﺮ ﺍﻟﻤﻠﻮﻙ".
ya'yan matar banza sunyi karya, sune sharrin sarakuna.
.
AMSA ga wannan maganar tasa:
gameda wannan amsar nake cewa muna da waqfat awannan gabar kamar haka:
.
1: ingancin wannan ruwayar ya tabbata kamar yanda yayi da'awa?.
WANNAN ruwayar dai imam attirmizy ya kawota asunan lamba:2226, kitabul fitan.
DA isnadi kamar hka:
ﺣﺪﺗﻨﺎ ﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻣﻨﻴﻊ, ﻗﺎﻝ: ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺳﺮﻳﺞ ﺑﻦ ﺍﻟﻨﻌﻤﺎﻥ, ﻗﺎﻝ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺣﺸﺮﺝ ﺑﻦ ﻧﺒﺎﺗﺔ, ﻋﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﻤﻬﺎﻥ, ﻗﺎﻝ ﺣﺪﺛﻨﻲ ﺳﻔﻴﻨﺔ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ:.....
wanda kuma kuma hashraj yayi tafarrudi ds qarin abunda sauran marawaitanta daga sa'id basu kawo ba, kamar yanda bayani zaizo agaba.
.
* SUWANENE WADANDA SUKA RAWAICETA DAGA SA'ID?
.
SHAIKHUL ISLAM IBN TAIMIYYA- wanda ake karyar an karance litattafansa- yake cewa:
ﻫﻮ ﺣﺪﻳﺚ ﻣﺸﻬﻮﺭ ﻣﻦ ﺭﻭﺍﻳﺔ ﺣﻤﺎﺩ ﺑﻦ ﺳﻠﻤﺔ ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻮﺍﺭﺙ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﻭﺍﻟﻌﻮﺍﻡ ﺑﻦ ﺣﻮﺷﺐ ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻋﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﻤﻬﺎﻥ ﻋﻦ ﺳﻔﻴﻨﺔ ﻣﻮﻟﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ)(, ﺭﻭﺍﻩ ﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﻦ ﻛﺄﺑﻲ ﺩﻭﺍﺩ ﻭﻏﻴﺮﻩ...
majmu'ul fatawa 35/12 bugun maktabatus safa.
.
* indai mutum dagasken ya karanta wannan gurin kuma yana da masaniya da ilimin rijal kamar yanda yake kurari babu yanda za ayi ya inganta ruwayar hashraj ba tare da ya dubi sauran hanyoyinba.
.
RUWAYAR awam bnil haushab, ibn Adiy ya kawota cikin al kamil 3/237.
.
RUWAYAR Abdul waris bn sa'id AHMAD ya rawaito ta 5/220, dayalisiy 2/162.
.
RUWAYAR hammad duba: mawariduzzam an lamba 1534.
.
Idan kaduba hashiyarsa tun dga shafi na 96-100 ya tattauna hanyoyin wannan hadisinne.
IBN ADIY yace akwai yahya bn ABI dalha shima dukkan wadannan da muka ambata sun rawaici wannan hadisin daga sa'id bn jumhan kamar yanda hashraj ya rawaita.
al kamil 3/372.
.
INA matsalar take?
.
WANNAN hadisin dawannan ziyadar bai tabbata ba:
ﻗﺎﻝ ﺳﻌﻴﺪ: ﺑﻨﻲ ﻣﻴﺔ ﻳﺰﻋﻤﻮﻥ ﺍﻟﺨﻠﺎﻓﺔ ﻓﻴﻬﻢ, ﻗﺎﻝ: ﻛﺬﺑﻮﺍ ﺑﻨﻮﺍ ﺍﻟﺰﺭﻗﺎﺀ.
WANNAN ziyadar hashraju shi kadaine yarawaitota daga sa'id - duk wadanda muka ambata abaya bau kawo wannan karinba- sanannen abune kuma indai hashraju yayi tafarrudi da rawaito abu to ruwayar bata inganta.
.
IBN hibban yace:
ﻣﻨﻜﺮ ﺍﻟﺮﻭﻳﺔ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺮﻭﻳﻪ, ﻟﺎ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻟﺎﺣﺘﺠﺎﺝ ﺑﺨﺒﺮﻩ ﺇﺫﺍ ﺍﻧﻔﺮﺩ.
al majruhin 1/277, lamba 288.
.
don haka ruwaya ce mara inganci balle kuma akafa hujja da ita azagi bayin ALLAH.
.
2: KAMAR YANDA MUN KAWO MAGANARSA CEWA YAYI "sa'idu bn jahman" WANNAN KUSKURE NE- tunda shine mai gyarawa mutane dabdi da asma u.. akwai kusakurai biyu anan:
.
1: bn jahman ﺟﻬﻤﺎﻥyace, alhali kuma bn JUMHAN ne.. ﺟﻤﻬﺎﻥ.
.
2: idan mun bishi a jahaman dinma to akwai kuskurai domin jumhanne-bidammil jim- sabanin yanda yakawo -bifathiha.
IDAN kuma akwai wadanda suka kawoshi ayanda yakawo muna jira akawo mana gurin, tunda ai kowane littafin ya karanceshi; don ko ibn taimiyyah jumhan yakawo shi ba jahmanba.
.
3: dayatashi karanto ruwayar cewa yayi:
ﻛﺬﺏ ﺑﻨﻮﺍ ﺍﻟﺰﺭﻗﺎﺀ.
)kazaba(.
wanda kuma ni dai adan iya bina banga inda aka kawo shi dahaka ba- sai yataimaka mana yafada mana bugun wacce maktaba yayi amfani dashi domin mubi muganewa idanuwarmu - ni kam na duba bugu kala biyu na sunan din dakuma sharhinsa amma abunda nagani shine:
ﻛﺬﺑﻮﺍ ﺑﻨﻮﺍ ﺍﻟﺰﺭﻗﺎﺀ.
)kazzibuu(.. muna jira yafada mana da wanne bugun yayi amfani har yasamu hakan kamar yanda yakaranta.
.
4: DAYATASHI fassara ﺑﻨﻮﺍ ﺍﻟﺰﺭﻗﺎﺀ sai yace:
"ya'ya'n matar banza".
TAMBAYA anan itace: a ina yaga wannan fassarar dayayi? BANUZZARQA'I daman yana nufin matar banza alarabci? YAFADA mana muji.
.
KAFIN yazo mana dawannan amsar bari nadan bamu abunda nagani:
)ﻛﺬﺑﻮﺍ ﺑﻨﻮﺍ ﺍﻟﺰﺭﻗﺎﺀ(
ﻫﻮ ﻣﻦ ﺑﺎﺏ ﻛﻠﻮﻧﻲ ﺍﻟﺒﺮﺍﻏﻴﺚ, ﻭﺍﻟﺰﺭﻗﺎﺀ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻣﻦ ﻣﻬﺎﺕ ﺑﻨﻲ ﻣﻴﺔ, ﻗﺎﻟﻪ ﻓﻲ ﻓﺘﺢ ﺍﻟﻮﺩﻭﺩ.
duba: tuhfatul ahwaziy 6/396 lamba 2226.
SAURAN bayanan awannan nuqdar muna jira idan aka bamu amsar tambayarmu zamuyi shi.
.
5: lokacin dayake karantowa cewa yayi:
"ﺑﻞ ﻫﻢ ﺷﺮ ﺍﻟﻤﻠﻮﻙ".
wanda kuma wannan ha incine tunda dai asali ba ahaka aka kawo shiba, ga yanda yafadi kamar yanda shi tirmiziy yakawo din:
"ﺑﻞ ﻫﻢ ﻣﻠﻮﻙ ﻣﻦ ﺷﺮ ﺍﻟﻤﻠﻮﻙ".
TAMBAYA anan: me yaci sauran abunda yacire daga cikin lafazin?? KO daman hakan ba matsala ababin naqali?? KO kuma nuskhar gurinsa ce ahaka? IDAN bugun dayayi amfani dashine ahaka to yafada mana madba'ar muje muduba.
* ko dai inda yakwafone shima aka rubuta ahaka shi kuma bai koma asalin littafinba.. oho dai.
6: da'awar shi'ancinsa ta fito qarara, ga fa abunda yake cewa:
"SAYYADI ALI YAZO YAGYARA KUJERAR ANNABTA WADDA YATARAR AN BA TA TA) TA SAKWARKWACE(
tambaya anan: suwane suka sakwarkwata ta din kenan?? S. ABUBAKAR da Umar da USMAN sune dai suka gabaci s. ALI ahalifanci kowa ya sani, yafito yayi byani me yake nufi muji.
NIDAI wallahi tuni nace gwandama adaina shakka akan shi'ancin wannan mutumin fa.
7: SAYYADI usmanu dinma an daina ragawa kenan? TUNDA dai cewa yayi " bisafitin a~mmah ba'ayi mutumin kirki acikinsuba.
WANNAN ataqaice kenan!!
zamu cigaba!!




FITOWA TA ) 17 (.SHIN YA TABBATA MANZON ALLAH)S.A.W( YA LA'ANCI MU'AWIYA??
.
Awajen bada amsar wannan tambyar nake cewa bai inganta cewa manzon Allah ya la'anci mu'awiyaba.. sannan hadisan da ake kawowa awajen nuna cewa annabi s.a.w ya la'anci mu'awiya sukan zama dayan wadannan:
.
* hadisanda babu ambaton mu'awiya acikinsu sannan kuma dukda haka basu ingantaba.
.
** hadisanda akwai ambaton mu'awiyan acikinsu amma kuma basu tabbataba.
.
*** hadisanda a iya cewa sun inganta to amma kuma babu ambaton mu'awiya acikinsu kamar yanda zaizo cikin raddin shubuhohin monitan kowaye..
Akwai hadisai nakarya da aka rawaito da dama awannan fagen amma zan takaitu wajen raddin wadanda monita yakafa hujja dasu tareda sauran lafuzzanda sukazo tahanyarsu.
.
NADAYA:
.
MONITA ya kafa hujja da hadisin:
ﻟﻌﻦ
ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻘﺎﺋﺪ ﻭﺍﻟﺴﺎﺋﻖ ﻭﺍﻟﺮﺍﻛﺐ...
yace :annabi yace ALLAH yatsinewa mu'awiya.
.
•••• ni kuma nake amsa masa dacewa:
.
'farko dai wannan hadisin yana cikin musnad na bazzar 9/286 lamba 3839..dakuma majma'u 1/113 lamba 436:
isnadinsa shine:
ﺍﻟﺴﻜﻦ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﻗﺎﻝ ﻧﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺼﻤﺪ, ﻗﺎﻝ ﻧﺎ ﺑﻲ ﻭﺣﺪﺛﻨﺎ ﺣﻤﺎﺩ ﺑﻦ ﺳﻠﻤﺔ, ﻋﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺟﻤﻬﺎﻥ ﻋﻦ ﺳﻔﻴﻨﺔ.
abu nabiyu :
wannan hadisin sam babu ambaton mu'awiya acikinsa, wanda kuma awannan babin ana bukatar nassi sahihi sarihi wanda shine zai zama abin dogaro.
.
NA uku:
ﺍﻟﺴﻜﻦ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ majhuline...
HAISAMI yafada amajma'u 7/395:
ﺍﻟﺴﻜﻦ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ ﻟﻢ ﻋﺮﻓﻪ.
idan kuma akwai wnd yayi karo dacewa yasamu tausiqi to yataimaka mana dagurin.
.
Na hudu:
akwai nakara acikin matanin hadisin; domin manzon Allah s.a.w yace:
ﻟﺎ ﻳﻜﻮﻥ ﺍﻟﻠﻌﺎﻧﻮﻥ ﺷﻔﻌﺎﺀ ﻭﻟﺎ ﺷﻬﺪﺍﺀ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ.
to ya kuma zamu ga annabin shine yake yin tsineneniya bayan ya nuna rashin kyawunta yakuma korewa masu yinta ceto ranar alkiyama??
.
Abu nabiyar:
awasu lafuzzan nasa yazo da:
ﻟﻌﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﺎﻣﻞ ﻭﺍﻟﻤﺤﻤﻮﻝ....
wanda tsinuwar tahau har kan dabbar data dauko shi wanda aka tsinewa, kuma idan mukayi la'akari zamuga manzon Allah s.a.w ya kyamaci tsinewa dabba, watarana wanj mutumi ya la'anci dabbarsa sai manzon Allah yai umarni da asauke kayan dasuke kanta sakamakon tsinemata da mai ita yayi, to ya kuma anan za a nuna cewa shi ma'aiki dakansa ya tsinewa dabbar??
.
WANNAN KENAN.
.
SANNAN WANNAN LAFAZIN YAZO CEWA:
.
ALIYYUL aqmar sunje gurin ibn umar suka tambayeshi wai dagaskene yaji manzon ALLAH yace: ﻟﻌﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻘﺎﺋﺪ ﻭﺍﻟﺴﺎﺋﻖ ﻭﺍﻟﺮﺍﻛﺐ??
sai ya amsa musu dacewa indai baiji annabi ya fadi ba to Allah yasa kunnuwansa sudaina ji kamar yanda yadaina gani, yace :
"ﻭﺇﻟﺎ ﻓﺼﻤﺘﺎ ﺫﻧﺎﻱ ﻛﻤﺎ ﻋﻤﻴﺖ ﻋﻴﻨﺎﻱ".
WANDA kuma itama bata ingantaba saboda acikin isnadinta akwai:
1:
ﻧﻀﺮ ﺑﻦ ﻣﺰﺍﺣﻢ wanda matrukine kuma dan shi a ne ,
IBN abi hatim yace: matrukine.
DUBA : aljarhu watta'adil 8/468.
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻘﻴﻠﻲ: ﻛﺎﻥ ﻳﺬﻫﺐ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺘﺸﻴﻊ.
addu'afa u 4/300.
2:
ﺗﻠﻴﺪ ﺑﻦ ﺳﻠﻴﻤﺎﻥ ﺍﻟﻜﻮﻓﻲ:
shi kuma maqaryacine, imamunnasa'i ya raunanashi, uqailiy kuma ya naqalto cewa maqaryacine.
DUBA: addu'afa u 1/155.
don haka bai ingantba ta kowacce fuska.
.
NAKE cewa kuma: idan ban manta ba ai nataba jin sarkin dakansa yace shi ba ya karbar hadisan hammadu... idan kuwa ya tabbata ya fadi hakan to ai ya hutar damu anan babinma domin wannanma hadisin hammadune; don haka mai yasa yakafa hujja dashi anan?? KO daman qa'idar tason raice ba a ko ina take aiki ba?? KO dai mantawa yayi da qa'idar kasancewa aruyawar yana da abunda yake son tabbatarwa??
.
SAI RUWAYAR DABARANI WADDA YASAKE KAFA HUJJA DA ITA:
ﻟﻌﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻘﺎﺋﺪ ﻭﺍﻟﻤﻘﻮﺩ...
wadda insha allahu bayanin bacinta zai zo arubutu nagaba.
ZAMU cgb!




FITOWA TA (18).
SHIN YA TABBATA MANZON ALLAH(S.A.W) YA LA'ANCI MU'AWIYA??
CI GABA!!
.
RUWAYA TABIYU DA SARKIN KOWAYE YAKAWO ITACE:
ﻟﻌﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻘﺎﺋﺪ ﻭﺍﻟﻤﻘﻮﺩ, ﻭﻳﻞ ﻟﻬﺬﻩ ﺍﻟﺄﻣﺔ ﻣﻦ ﻓﻠﺎﻥ ﺫﻱ ﺍﻟﺈﺳﺘﺎﻩ....
WANDA KUMA RUWAYAR TAZO DA LAFUZZA MABANBANTA, ITAMA KUMA KAMAR WADDA TAGABATANE...
dabaraniy ya kawota cikin al mu'ujamul kabir 17/176 lamba 465.
Haithami ya kawota cikn majma'u 5/242 lamba 9237 yakumace dabaraniy ne yarawaito ta.
IBN abi asim ya kawota da lafazin:
ﻟﻌﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻘﺎﺋﺪ ﻭﺍﻟﻤﻘﻮﺩ ﺑﻪ.
1: BABU AMBATON MU'AWIYA ACIKINTA; DMN CEWA AKAYI:
ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺨﻂﺐ ﻋﻠﻰ ﻣﻨﺒﺮﻩ ﻓﻘﺎﻡ ﺭﺟﻞ ﻓﺄﺧﺬ ﺑﻴﺪ ﺍﺑﻨﻪ ﻓﺄﺧﺮﺟﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ, ﻓﻘﺎﻝ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(
)...
DON HAKA MENENE HUJJAR CEWA RAJULUN DINNAN MU'AWIYANE?? IDAN MA FA RUYAWAR TA TABBTA KENAN.
2: NADR YA RAWAICETANE DAGA MAHAIFINSA ASIM BN AMRU, SHI KUMA ASIM DIN AKWAI SABANI KAN KASANCEWARSA SAHABI, KAMAR YANDA IMAM AHMAD YAFADI.
ﻟﺎ ﺩﺭﻱ ﺳﻤﻊ ﻣﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ.
AWANI GURIN KUMA, KAMAR YANDA YAKE CIKIN AL ISABA 3/574, BAGAWIY YACE:
ﻟﺎ ﺩﺭﻱ ﻟﻪ ﺻﺤﺒﺔ ﻟﺎ.
3: AKWAI NAKARA ACIKIN MATANIN HADISIN.
SHAIKHUL ISLAM YAYI MAGANA KAN NAKARAR HADISIN CKN MINHAJUSSUNNAH 4/445, JUMULLAR MAGANAR TASA ITACE:
sanannen abune ma'aiki(s.a.w)yana yin khudubobi a jumu'a da idi dakuma sanda wani abun yafaru,kuma mu'awiya da mahaifinsa suna halartarsu;don haka anan dayan biyune:
ko dai yazama duk khudba idan ma'aiki zaiyi tashi suke sufita ba sa saurara... ko kuma yazama suna zaunawa susaurara awannan karonne suka tashi suka fice-kmr ynd ita wannan ruwayar maras inganci tanuna-.
idan kace ai basa zma tashi suke suyi ficewarsu duk khudbah to anan ka soki annabi, bazai taba yuwuwa ace kullum tashi suke suyi fucewarsuba kuma annabi yarabu dasu ba tare da ya dau mataki kan hakanba.
idan kuma kace ai ranarne kadai suka tashi suka fice, to ananma akwai suka ga annabi dakuma rashin sanin ya kmt, suka ga annabi tayanda zai la'anci mutanenda duk khudbarsa suna zama don sun tashi rana daya sun fita wanda kuma ba'asan menene uzurinda yasa suka fitanba, alhali kuma ma'aiki ya siffantu da tausasawa dakuma kyautatawa wadanda ke tare dashi.
sannan kuma ahankalcema- tunda ku sarakan kafa hujja dashine- taya za ayi ace mutanenda kullum dasu ake khudbarnan rana daya kuma kawai sutashi suyi tafiarsu daga fara khudbar annabi??
ﻣﻨﻘﻮﻝ ﺑﺘﺼﺮﻑ.
IDAN KACE MINI DON ME ZANCE BABU AMBATON MU'AWIYA A RUWAYAR ALHALIN AN SIFANTA SHI DA ﺫﻭ ﺍﻟﺎﺳﺘﺎﻩ ARUWAYAR SAI NACE MAKA:
bayan illarda ruwayar take da ita akaron kanta to siffanta shi da zhul istahi din kansa ruwayar datazo dashi tanuna mu'awiyane hkn bata ingantaba,
BUKHARI ya kawota ckn: attarikh al kabir1/274da dabaraniy a ausadu dasanadi:
ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﺍﻟﻔﻀﻞ ﻋﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﻋﻦ ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﺍﻟﻜﻬﻴﻞ ﻋﻦ ﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﺑﻦ ﺍﻟﺒﺮﺍﺀ ﺑﻦ ﻋﺎﺯﺏ ﻋﻦ ﺑﻴﻪ
kuma tana da illoli biyar zuwa shida abarin sanadinta kadaima banda matani, zan ambaci wasun illolin..
1: SALAMATU bnil fadl Abu abdillahil abrash... da'ifine yana rawaito manakir daga ibn is'haq a magaziy, kmr ynd nasa'iy yafada ckn addu'afa u wal matrukun 1/47 lamba:241.
BUKHARI yace:
ﻋﻨﺪﻩ ﻣﻨﺎﻛﻴﺮ ﻭﻓﻴﻪ ﻧﻆﺮ.
add'afa us sagir lamba 152.
IBN hibban yakawoshi ckn al majruhin lamba 425.
duba: al mugni fiddu'afa i lamba 2543.
2: ABU IS'HAK Amru bn Abdillah assabi'iy yayi an ana ahadisn shi kuma daman ya shara dacewa yana tadlisi:
AL ala'iy yace:
ﺗﻘﺪﻡ ﻧﻪ ﻣﻜﺜﺮ ﺍﻟﺘﺪﻟﻴﺲ.
Duba: jami'ut tahsil 576.
IBN hajar yace:
ﻣﺸﻬﻮﺭ ﺑﺎﻟﺘﺪﻟﻴﺲ.
duba: ta'arifu ahlittaqdis lamba 91.
3: IBRAHIM bnil bara'i majhuline, bukhari yakawo tarjamarsa cikin attarikul kabir lamba 864 bai kuma wassaqa shiba... baza ayi izina da tausiqinda ibn hibban yayi masaba sbd mutasahiline shi, sannan kuma babu wanda ya wafaqa masa akan tausiqin.
4: imamul bukhari yace:
ﻳﺨﺘﻠﻔﻮﻥ ﻓﻲ ﺳﻨﺎﺩﻩ.
duba: tarikh lamba 884.
DON haka akwai ibdirabi acikin sanadin ruwayar.
TAZO da ambaton ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﻛﻬﻴﻞ awasun hanyoyin kuma babu ambatonsa.
TA kuma zo da lafazin:
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻋﻠﻴﻚ ﺑﺎﻟﺄﻗﻴﻌﺲ.
bara u yatambayi mahaifinsa:
ﻣﻦ ﺍﻟﺄﻗﻴﻌﺲ??
SAI yace mas:
ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ.
Itama kuma bata ingantaba, akwai nadru bn muzahim a sanadinta wanda kuma matrukine kuma dan shi'ane:
uqailiy yace:
ﻛﺎﻥ ﻳﺬﻫﺐ ﻟﻰ ﺍﻟﺘﺸﻴﻊ.
DUBA: al jarhu watta'adil 4/300.
ATAKAICE dai kamar yanda nafadi amuqaddima ta babu wani hadisi ingantacce da annabi (s.a.w) yala'anci mu'awiya acikinsa, idan kuma akwai to muna jira akawo.
Zamu cgb!!




FITOWA TA )19(.
SHIN ANNABI YACE MU'AWIYA ZAI MUTU BA AKAN SUNNAH BA??
.
SARKIN KURI YACE: gashi hadisi yazo dayake nuna mu'awiya zai mutu ba akan musulunciba...
"ﻳﻂﻠﻊ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺭﺟﻞ ﻣﻦ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻔﺞ ﺭﺟﻞ ﻳﻤﻮﺕ ﻋﻠﻰ ﻏﻴﺮ ﻣﻠﺘﻲ"..
wani mutumi dazai mutu ba a kan sunnah ta ba zai bullo muku ta wancan rangon.,
.
SAI ABDULLAHI BN AMR YACE:
ﻭﻗﺪ ﻛﻨﺖ ﺗﺮﻛﺖ ﺑﻲ ﻗﺪ ﻭﺿﻊ ﻟﻪ ﻭﺿﻮﺀ ﻓﻜﻨﺖ ﻛﺤﺎﺑﺲ ﺍﻟﺒﻮﻝ ﻣﺨﺎﻓﺔ ﻳﺠﻓﻂﻠﻊ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ...
daman na bar mahaifina an kai masa ruwan alwala, sai nazam tamkar wanda yake riqe fitsari alhalin ya matseshi;sbd tsoron kada mahaifina yazama shine wannanda zai bullo din, sai kwa gashi mu'awiya ya bullo...
.
NI kuma MISBAHU NAKE CEWA:
wannan tatsuniyar sam bata ingantaba, tazo cikin ANSABUL ASHRAF 5/134. DA SANADI KAMAR Haka:
1:ﺣﺪﺛﻨﻲ
ﺳﺤﺎﻕ ﻭﺑﻜﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﻬﺜﻴﻢ ﻗﺎﻟﺎ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺯﺍﺑﻦ ﻫﻤﺎﻡ ﻧﺎ ﻣﻌﻤﺮ ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻃﺎﻭﺱ ﻋﻦ ﺑﻴﻪ ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺎﺹ ﻗﺎﻝ:....
2:ﺣﺪﺛﻨﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ ﺣﺪﺛﻨﻲ ﻳﺤﻴﻰ ﺑﻦ ﺍﺩﻡ ﻋﻦ ﺷﺮﻳﻚ ﻋﻦ ﻟﻴﺚ ﻋﻦ ﻃﺎﻭﺱ ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ..,
.
FARKON ABUN DUBAWA SHI KANSA ALBALAZURIY WANDA YA RAWAITO TA ABUN DUBAWA NE, BABU WANDA YA WASSAQA SHI CIKIN MALAMAN MUSULUNCI., WANNAN KENAN.
.
malamai sunyi bayanin bacin wannan ruwaya amabanbantan gurare, misali: duba: almuntakhab minal ilal lamba 136 akwai ishararda ke nuni bisa bacin ruwayar.
.
BAYANIN ILLOLINTA.
.
*hanya ta farko:
acikinta akwai ABDURRAZAQ BN HUMAM tare da girman matsayinsa amma yana da matsaloli kamar haka:
.
1: akwai matsala cikn abubbanda aka rawaita agurinsa akarshe.
NASA'I yace:
ﻓﻴﻪ
ﻧﻆﺮ ﻟﻤﻦ ﺣﺪﺙ ﻓﻴﻪ ﺑﺎﺧﺮﺓ.
addu'afa u wal matrukun lamba 379.
2: akwai kusakurai cikin ruwayoyinda yadogara da haddarsa wajen badasu SANNAN kuma akwai shi'anci atare dashi.. kamar ynd ibn hibban yafadi ckn ASSIQAT lamba14146.
3: ya sami ikhtiladi kuma yana karbar talqini.
don haka ruwayoyinsa da basa cikin littafinsa akwai matsala akansu.
bukhari yace:
ﻣﺎ ﺣﺪﺙ ﻣﻦ ﻛﺘﺎﺑﻪ ﻓﻬﻮ ﺻﺢ.
attarikh lamba 1933.
.
WANDA KUMA WANNAN RUWAYAR TANA NAN BANGAREN; ASABIDA HAKAN BATA INGANTABA.
.
**hanya ta biyu:
1: sharikh bn Abdillah al qadiy.
yana da rauni, haddarsa ta sami matsala ba ma daga sanda yakarbi alqalanci.
IBN ADIYY yace:
ﺳﻴﺊ ﺍﻟﺤﻔﻆ ﻣﻀﻂﺮﺏ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻣﺎﺋﻞ.
al kamil lamba 888.
yana kuma da manakir cikin ruwayoyi.. duba mizanu lamba 3697.
2: laisu bn abiy sulaim.
YA sami ikhtiladi har yazam baima san abnd yake fadi ba.. kamar yanda ibn hibban yafadi:
ﺍﺧﺘﻠﻄ ﻓﻲ ﺍﺧﺮ ﻋﻤﺮﻩ ﺣﺘﻰ ﻛﺎﻥ ﻟﺎ ﻳﺪﺭﻣﺎ ﻳﺤﺪﺙ ﺑﻪ, ﻓﻜﺎﻥ ﻳﻘﻠﺐ ﺍﻟﺄﺳﺎﻧﻴﺪ ﻭﻳﺮﻓﻊ ﺍﻟﻤﺮﺍﺳﻴﻞ ﻭﻳﺄﺗﻲ ﻋﻦ ﺍﻟﺜﻘﺎﺕ ﺑﻤﺎ ﻟﻴﺲ ﻓﻲ ﺣﺪﻳﺜﻬﻢ.
al majruhin lamba906.
NASA'i yace: da'ifun.
DUBA: addu'afa u wal matrukun.
DUBA: al mugni fiddu'afa i lamba 1617.
AQARSHE KUMA: sarkin kuri ya raunanashi dafadinsa: duk banu umayya mutanen banzane babu wani nakirki acikinsu..
KUMA wannan rawin dai idan kakoma tarjamarsa cikin al kamil fi du'afa ir rijal lamba: 1617, zakaga ance:
ﺍﻟﺄﻣﻮﻱ.....
don haka dai bata ingantaba.
.
MANHAJINMU SHINE: AIKI DA INGANTACCIYAR RUWAYA, DA KOWACCE RUWAYA IDAN TAZO KAWAI KARBA AKE TO DA SAI MUCE MUKU:
.
Ai an rawaito hadisi da irin wannan sigar ma'aiki yace : dan aljanna zai bullo sai gashi mu'awiya yabullo, haka yasake maimaituwa har tsawon kwana uku.
.
ABU NU'AIM YA KAWO CIKIN HILYA 10/385, LAMBA 15689 suna mai lamba 685)IBRAHIM BN ISAH( DA SANADI HAR ZUWA IBN UMAR, MA'AIKI YACE:
"ﻳﻂﻠﻊ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺭﺟﻞ ﻣﻦ ﻫﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ" ﻓﻂﻠﻊ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ, ﺛﻢ ﻗﺎﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﻐﺪ ﻣﺜﻞ ﺫﻟﻚ ﻓﻂﻠﻊ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ, ﺛﻢ ﻗﺎﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﻐﺪ ﻣﺜﻞ ﺫﻟﻚ ﻓﻂﻠﻊ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ.
Shi yasa ibn adiyy cikin al kamil lamba:464 yai nuni kan rashin ingancinta.
.
* koda akwai ingantattun ruwayoyi dasuke nuna cewa mu'awiya dan aljannane, sabanin wannan wadda muka rushe datake nuna cewa dan wutane.
.
ATAKAICE DAI WACCAN RUWAYA DAKE NUNA CEWA DAN WUTANE BATA INGANTABA SANADAN WA MATANAN.
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ.
ZAMU CIGABA.





*Koma Saman Shafi*

*New Update*
12345»

→Online People 1
→Adadin Maziyarta 30412

*Bayyana Ra'ayin ka*

*Home / Gida*



MisbahuAbudullah 1 1

Snack's 1967